Wani Miji Ya Silale Cikin Asibiti Kawai Domin Tarawa Da Matarshi Mai Jinya

0
623

 

Daga Usman Nasidi

 

WANI mutumi dan kasar Zimbabwe na hannun hukuma sakamakon silalewa dakin marasa lafiya mata a asibitin Masyingo misalin karfe 3 na safe domin tarawa da matarsa dake kwance a asibitin.

Mutumin wanda shahararren mai sayar da abinci a cikin garin yayi sa’insa da ma’aikatan asibiti cikin dare dan sun hanashi ganin matarsa.

Daga karshe ya samu shiga asibitin kuma ya tara da matarshi a gaban sauran marasa lafiya goma dake cikin dakin.

Shugaban asibitin, Amadeus Shamu, ya tabbatar da faruwan wannan abu ga jaridar iHarare kuma yace asibitin sun fara gudanar da bincike.

Shamu yace: “Misalin karfe 3 na dare marasa lafiya masu jinya suka fara damuwa da karan wasu masu Tarawa da juna. Sai ma’aikatan asibitin suka kira jami’an tsaro su fitar da mutumin daga asibitin.”

Binciken da aka gudanar na nuna cewa matar na tsoron mijin ne kuma idan taki yarda ya tara da ita zai iya dukanta cikin jama’a duk da rashin lafiyanta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here