Ya Maka Surukinsa A Kotu Bisa Zarginsa Da Sace Masa Mata

0
569

 

Daga Usman Nasidi

 

A RANAR Talata ne wani magidanci mai shekaru 35, Haruna Ali, ya yi karar surukinsa, Adamu Mai-Takalma a kotun Shari\’a II dake zamanta a Magajin Garin Kaduna bisa zarginsa da sace masa mata.

Mai shigar da karar ya shaidawa kotu cewa mai dakinsa, Hadiza Haruna, ta bar dakinta na aure ta tafi gidan iyayenta ba tare da izininsa ba.

Ya yi ikirarin cewa matarsa ta kwashe watanni 11 tana zaune a gidan iyayenta da sunan tana jinyar rashin lafiya.

\”Ina rokon kotu ta taimaka ta dawo min da mata na kuma na dauki alkawarin zan kula da ita ko wace irin rashin lafiya take fama da ita,\” inji Haruna Ali.

A nasa bangarensa, mahaifin Hadiza ya shaidawa kotu cewa diyarsa tayi barin ciki sau biyu cikin watanni 11 kuma hakan ya janyo ta kamu da ciwon yoyon fitsari wanda a turance yiwa lakabi da (VVF).

\”Diyata ta dawo gida ne saboda tayi barin ciki. \”Ta kwashe watanni biyar a gida na amma mijinta bai zo ya duba lafiyarta ba. \”Ni da kaina na mayar da ita gidan mijinta amma daga baya na samu labarin cewa lamarin ya tsananta har bata iya rike fitsari,\” inji Mai-Takalma

Har’ila yau, Mai Takalma ya yi ikirarin cewa diyarsa ta nemi izinin mijinta kafin ta taho gidansa kana ya ce a halin yanzu bata shirya komawa gidan mijinta ba.

Ya fadawa kotu cewa lafiyar diyarsa yafi muhimmanci fiye da aurenta kuma har yanzu tana karbar magani.

Alkalin kotun, Musa Sa\’ad ya umurci a canja wa Hadiza asibiti idan zata samu kulawar kwararu kuma ya umurci mijinta ya biya kudin maganin.

Sannan ya dage shari\’ar zuwa ranar 11 ga watan Satumba inda yace zai yanke hukunci bayan an kawo masa sakamakon binciken likitoci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here