Daga Usman Nasidi
Yayin gudanar da zaben 2019, hukumar gudanar da zabe ta kasa mai zaman kanta wato INEC za ta ciyar da yan sandan da zatayi amfani da su wajen zabe da kudi naira biliyan shida.
Wannan na kunshe cikin kasafin kudin da hukumar INEC ta mikawa majalisar wakilai a ganawarsu ta yau.
Yan majalisan sun tada jijiyoyin wuya kan wadannan bukatu da shugaban hukumar INEC, Farfesa Mahmoud Yakubu, ya gabatar.
Rahotanni sun bayyana cewa Kwamitin majalisar wakilan tarayya kan harkokin gudanar da zaben sun shiga ganawa da jami’an hukumar gudanar da zabe ta asa mai zaman kanta wato INEC da safen nan a zauren majalisa.
Shugaban hukumar INEC, farfesa Mahmoud Yakubu, ne ya jagoranci sauran jami’an hukumar domin muqabala kan bukatan kudin da suk mika na gudanar da zaben 2019.
Kwamitin karkashin jagorancin Mrs Aisha Dukku zasu yi tambayoyi don tabbatar da gaskiyan abubuwan a hukumar INEC ta bukaci yi da kudi sama da Biliyan N240bn.