Isah Ahmed, Jos
SHUGABAN kungiyar yakin neman zaben shugaban kasa Muhammad Buhari [BCO] na kasa Alhaji Danladi Garba Fasali ya yi barazanar cewa, matukar shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki bai sauka daga kan mukaminsa na shugaban majalisar dattawa ba, ‘yan kungiyar su za su mamaye harabar majalisar. Alhaji Danladi Pasali ya bayyana haka ne a garin Abekuta ta jihar Ogun, a lokacin da yake jawabi a wajen kaddamar da sakatariyar kungiyar reshen jihar.
Danladi Pasali da yake tare da mataimakin shugaban kungiyar Dokta Salam da shugaban kungiyar na jihar Ogun Adeke Bada tare da sauran shugabannin kungiyar na yankin jihohin kudu masu yamma da dubban mutanen da suka canza sheka daga jam’iyyar PDP suka koma jam’iyyar APC.
Ya yi bayanin cewa mu kungiyar yakin neman zaben shugaban kasa Buhari muna bukatar shugaban majalisar dattawan Bukola Saraki ya sauka daga kan mulaminsa, tun da ya fita daga jam’iyyar APC ya koma jam’iyyar PDP.
‘’Ya kamata Saraki ya yi koyi da abin da shugaban marasa rinjaye na majalisar dattawa Sanata Godswill Akpabio ya yi na sauka daga kan mukaminsa, bayan da ya canza sheka daga jam’iyyar PDP ya koma jam’iyyar APC. Mun yi tsammanin cewa Saraki zai yi haka, idan bai yi haka ba, zamu mamaye harabar wannan majalisa domin mu ga cewa ya sauka.’’
Ya ce wadanda suka nuna sha’awar tsayawa takarar kujerar shugabancin kasar nan a zaben shekara ta 2019, ba zasu iya kayar da shugaba Muhammad Buhari ba.