Isah Ahmed, Jos
Shugaban kungiyar ci gaban al’ummar Fulani makiyaya ta Nijeriya ta Gan Allah Alhaji Sale Bayari, ya bayyana cewa shi bai taba ganin inda mutanen Arewa suka zauna da shugaban kasa Muhammad Buhari, suka roki ya yi masu wasu ayyukan raya kasa kamar hanyoyi mota ko asibitoci ba. Alhaji Sale Bayari ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi a wajen taron karramar da kungiyar daliban manyan makarantun arewa suka yi masa da Garkuwan matasan Arewa, a garin Jos babban birnin jihar Filato a karshen makon da ya gabata.
Ya ce a kullum mutanen yankin Neja Delta suna cewa a yi masu kaza, a yi masu kaza kuma su ce idan ba a yi masu ba, ba za a dauki mai ba.
Ya ce amma mu mutanen Arewa ba mu taba cewa idan ba a yi mana kaza ba, ba za a dauki masara da tumatur da shanu daga Arewa a kai kudu ba.
‘’A yankin Neja Delta akwai mutanen da basa aikin komai, amma in wata ya kare ana baiwa kowa Naira dubu 65. Yanzu a arewa muna da miliyoyin mutane da suke son a dauke su aikin da za a rika basu naira dubu 18, a wata. Yanzu idan ka je Ibadan za ka ga hanyar mota da ake yi. Kaje Asaba ka ga gadar da ake yi. Ana yi masu irin wadannan ayyuka ne saboda suna nema a yi masu’’.
Alhaji Sale Bayari ya ce ya kamata mutanen Arewa su rika fitowa suna mika bukatun abubuwan da suke son a yi masu. Shima shugaban Buhari ya kamata ya san cewa mutanen arewa suna sonsa, ta hanyar yi masu wasu abubuwa na ci gaba.
Alhaji Sale Bayari ya ce yaji mamaki da wannan kungiya suka san shi kuma suka san abubuwan da yake yi, har suka karrama shi da Garkuwan matasan Arewa. Don haka ya ce babu abin da zai ce kan wannan karramawa da aka yi masa, sai dai ya ce ya gode.