Masari Ya Rantsar Da Sabon Kwamishina

0
831
Gwamna Aminu Bello Masari
Mustapha Imrana Abdullahi Daga Kaduna
GWAMNAN Jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari ya rantsar da sabon kwamishinan da zai yi aiki a matsayin kwamishinan ayyukan musamman.
Alhaji Bashir Abdullahi Jibiya ne sabon kwamishinan da aka rantsar, jim kadan bayan rantsar da shi Gwamna Aminu Bello Masari ya ce jam\’iyyar APC a shirye take ta ta fi tare da dukkan masu bayar da gudunmawarsu domin ganin al\’amura sun ci gaba.
\”Ya jima yana kokarin bayar da gudunmawarsa musamman domin ganin APC ta samu nasarar da ake bukatar ta samu a Kowane fage\”.
Gwamna Masari ya ci gaba da cewa \” Hakika wannan bawan Allah ya yi Imani tare da amincewa da dukkan tsare tsare na shugaba Muhammadu Buhari, don haka lokaci ya yi da za a tuna da shi saboda ayyukan da yake yi tsawon lokaci\”.
Mutum ne da ya tsaya tsayin Daka lokacin da ake ta fafutukar ganin nasara ta samu.
Masari ya yi addu\’ar fatan Alkairi da kuma fatan Allah ya yi mana jagora baki daya.
Mataimakin Gwamnan Katsina, sakataren Gwamnati, Shugaban APC na Jihar tare da wadansu daga cikin mambobin majalisar zartaswa Jihar na daga cikin wadanda suka halarci taron rantsuwar

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here