Ya Jefar Da Kanwarsa Don Gudun Gori

0
761
Rabo Haladu Daga Kaduna
MASU unguwanni da dagatai na cikin shugabannin al\’umma wadnda a kan garzaya
wurinsu da yaran da aka tsinta, mai yiwuwa saboda tunanin da ake da shi cewa su ne suka fi sanin matsalolin al\’umma da hanyoyin magance su.
Alhaji Mai-Fada Ali, shi ne mai unguwar Gama B a yankin Brigade da ke birnin Kano, kuma
gidansa ya zama tamkar wata cibiya ta kai yaran da aka tsinta, inda daga nan shi kuma sai ya kai su wajen hakimi har a sada su da gidan marayu.
A dalilin irin yawan yaran da ake kai masa a kai-a kai, har ya kasance yana rikon biyu daga
cikinsu a yanzu haka.
Rakiba (ba sunanta na gaskiya ba), mai shekara 18, na daga cikin yara biyun da mai unguwa yake rikonsu, inda ya zame musu uwa da uba da danginsu.
Ya shaida wa manema labarai  cewa, \”An kawo ta cigiya majalisata ne a lokacin da ba ta wuce shekara biyu da haihuwa ba, aka ce a Layin Takari aka tsinto ta an ajiye ta tana ta kuka. Sai na karbe ta ta kwana washegari aka bai wa hukuma ita, amma sai wata mata ta bukaci a bata rikonta. Daga baya ta dawo da ita saboda ta fara fuskantar kalubale daga wajen dangin mijinta.
Mai unguwa dai ya nuna min wata takarda, wacce ya ce a shekarar da ta gabata ne wani
mutum ya aiko masa, a ciki yana ikirarin cewa shi yayan yayrinyar farko ne, kuma shi ne ya jefar da ita shekaru da dama da suka wuce.
Ya bayyana cewa ya yi hakan ne saboda azabar da dangin mahaifiyarsu ke gana mata bayan mutuwar uwar tasu, sakamakom zargin cewa ba ta hanyar aure ta haife ta ba.
Shi kuma kamar yadda ya ce a wasikar, ya yi kankantar da zai iya kare kanwar tasa daga
kalubalen da take fuskanta, shi ya sa ya yanke shawarar ajiye ta a inda ya san za a tsince ta, ya kuma bibiyi inda aka kai ta.
Sai dai wani abun jaje shi ne rashin sake bullowar wannan bawan Allah kamar yadda ya yi
alkawarin cewa zai koma ya dauki Rakiba.
\”Na jira dawowarsa amma har yau shiru ba amo ba labari shekara daya kenan da kawo wannan wasikar,\” a cewar Mai Unguwa.
A hirar da na yi da Rakiba dai ta shaida min cewa bayan an samu wannan wasika ta fara
murnar haduwa da danginta, amma da aka shafe lokaci yayan nata da ya aika wa Mai Unguwa wasikar bai dawo ba har aka shafe tsawon lokaci kamar yadda ya yi ikirari, sai jikinta ya yi sanyi.
\”A yanzu dai kam ina fatan idan har ina da rabon ganin jinina to Allah ya sada mu da alkhairi, idan kuma babu rabon ganawa to Allah ya kara min dangana, Baba Mai Unguwa ma ya ishe ni rayuwa, in ji Rakiba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here