Na Fito Takara Ne Domin Maganin Wadanda Suka Kasa – Adamu Kabir

0
700
Mustapha Imrana Abdullahi Daga Kaduna
MAI neman kujerar majalisar dokokin jihar Kaduna domin wakiltar mazabar Unguwar Sanusi, Alhaji Adamu Kabir Umar, ya bayyana wa manema labarai a Kaduna cewa ya fito takara ne da nufin bayar da gudunmawarsa a gyara abubuwan da wasu suka kasa.
Adamu Kabir ya bayyana hakan ne lokacin da yake ganawa da manema labarai a cibiyarsu da ke Kaduna.
\”Hakika akwai wadanda suka dade suna yin abubuwa da yawa na rashin gamsar da jama\’a, saboda haka mutane suka kuma sun fitar da ni sai na tsaya wannan takara domin in wakilce su a matsalar Kaduna ta yadda za mu rika gabatar da dokoki masu ma\’ana ga rayuwar jama\’a\”.
Jama\’ar wannan mazaba ta unguwar Sanusi sun san wadanda suka kasa saboda mazabar nan ta hada da yankuna hudu ne da suka hadar da kurmin Mashi, Badikko, Sabon Gari da Unguwar Sanusi duk sun Taru baki daya suka ce sai na fito wannan takara domin su samu kyakkyawan wakilci a majalisar dokokin jihar Kaduna.
Ya ci gaba da shaida wa manema labarai cewa akwai dokokin da suka kamata a gabatar a majalisa amma masu wakiltar jama\’a sun kasa yin hakan sai dai bangaren Gwamnati ne kawai suke aiwatar da aikin da yakamata na gabatar da dokoki
\”Akwai tsare tsare da na shirya aiwatarwa da suka hadar da kokarin samar da kyawawan dokokin kan hanya domin yin tukin ababen hawa a bisa doka, tsare tsare a kan al\’amuran barace barace da samar wa jama\’a ayyuka musamman ta hanyar koyar da su sana\’o\’i da za su Dogara da kawunansu.
Saboda haka muka yi wa wannan harkar neman zabe batun girma da arziki da ake wa lakabi Dan takara Magani sai da Gwaji, na Unguwar Sanusi

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here