Buhari Zai Ci gaba Da Daure Barayin Nijeriya

0
677
Mustapha Imrana Abdullahi
SHUGABAN kasar tarayyar Nijeriya Alhaji Muhammadu Buhari ya bayyana cewa ko shakka babu zai ci gaba da daure dukkan berayen kasar musamman wadanda suka kwashe dukiyar talakawa.
Ya dai bayar da wannan tabbaci ne a fadar shugaban kasar Nijeriya lokacin da ya dawo daga kasar Ingila bayan kwashe tsawon kwanaki goma yana hutu a can.
Ya ce kun san dama abin da ake tsammani daga gare ni kenan wato in yi maganin dukkan wani maha\’incin da ya kwashe dukiyar kasa,wato dai ma\’ana wadanda suka jefa talaka cikin matsala sakamakon kwashe dukiyar kasar.
In dai za a iya tunawa Nijeriya na fama da maha\’intan da suka kwashe kudin kasar suka Kai kasashen ketare amma kuma Talakawa masu dukiyar an bar su cikin muguwar akubar talaucin.wanda sakamakon hakan ne Talakawa suka makalewa Muhammadu Buhari suke zabensa a duk lokacin da aka zo zabe tare da tunanin Buhari zai yi maganin Yan Handama da Babakeren dukiyar al\’umma.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here