Mustapha Imrana Abdullahi Daga katsina
GWAMNAN Jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari, ya Gargadi Sababbin kantomomin rikon da ya Nada domin su jagoranci tafiyar da kananan hukumomin Jihar da kada su sake su rika tafiyar da harkokin Mulki daga wajen kananan hukumomin su.
Gwamna Masari ya yi wannan Kiran ne lokacin da yake jawabi a wurin rantsar da kantomomin rikon kananan hukumomi 34 da za su jagoranci al\’ummar kananan hukumomin su.
Masari ya shaidawa kantomomin cewa shi da kansa yakan Je Abuja ne idan akwai wani aiki ko abin da zai kaishi garin na Abuja.
\”Zai yi wahala haka kawai in yi tafiya zuwa kasashen waje don haka ne kullum Ina tare da jama\’a a nan katsina\”. Inji Masari.
Gwamnan ya ci gaba da cewa tun farko abin da yaso shi ne ayi zaben Shugabannin Kananan hukumomi tare da kansiloli su amma sai jam\’iyyar PDP ta Kai Gwamnatin APC kotu.
Ya yi bayanin cewa duk da yake duk da yake sun samu nasara a kotun amma Yan adawa sun ta fi kotun daukaka aka a Kaduna.
Ya ce sun fahimci cewa manufar zuwa kotun itace a hana APC samar da tsarin shugabanci a matakin kananan hukumomi.
Gwamnan ya ce koda yake ya yi alkawarin ba zai taka Doka ba amma a cikin wani yana yi dole a lankwasa domin samar da wadannan kantomomi a matakan kananan hukumomi 34 na Jihar
Gwamnan ya kuma bayar da tabbacin cewa Mafi yawan mutanen da aka Nada bai San su ba, amma yana fatar za su yi aiki domin ci gaban jama\’a gwargwadon ikonsu.
Ya ankarar da jama\’a cewa batun tantancewar da aka yi an yi ne domin cika sharuddan doka
Sai dai ya ankarar da su cewa irin yadda suka aiwatar da ayyukan su ga jama\’a zai tabbatar masu da irin yadda za su kasance nan gaba.
\”Kodayake za ku samu asusun kananan hukumomin da kusan Babu komai, duk da haka ya zama wajibi kuyi aiki da gaskiya tare da rikon Amana ta hanyar irin yadda zaku ririta dan abin da yake aljihun kananan hukumomin ku\”.
Gwamnan ya kuma yi gargadi ga dukkan shugabannin kantomomin rikon da kada su sake su wuce Gona da iri, kada Wanda ya sake a shiga mulki da irin wannan niyya
\”Ba Zai dauki koda minti daya ko dakika guda ba wajen Cire duk wani da aka samu da laifi wajen gudanar da aikinsa.
Gwamnan ya kuma shawarci kantomomin da tabbatar sun yi aiki tare da shugabannin jam\’iyya cikin kwanciyar hankali da lumana da juna.
Su kuma yi aiki da tsare tsare da kuma tanaje tanajen tsarin aikin kananan hukumomi.
Gwamnan ya yi alkawarin cewa zai Tallafa masu da kudi ta yadda za su samu sukunin gudanar da aiki cikin nasara.
Bikin rantsuwar ya samu halartar mataimakin Gwamna AlhajiThe Mannir Yakubu, kakakin Majalisar dokokin Jihar katsina Alhaji Yahaya Abubakar Kusada da sakataren Gwamnatin Jihar Dakta Mustapha Inuwa da kuma Dan kasuwa Alhaji Dahiru Bara\’u Mangal sauran jama\’ar da suka halarci bikin sun hada da Yan kasuwa,mambobin majalisar dokokin Jihar da na zartaswa da kuma Yan siyasa da dama.