Shanu Da Raguna Sun Yi Sauki A Kasuwannin Kano

0
901

JABIRU A HASSAN,Daga Kano.

Farashin shanu da raguna yayi kasa a kasuwannin jihar kano duk da cewa gwamnatin jihar ta biya albashin wannan wata na Agusta kwanaki kadan kafin Sallah.
Wakilinmu wanda ya ziyarci wasu kasuwannin kauyuka a jihar, ya ruwaito cewa shanu da raguna da awaki suna sauki sosai idan aka yi la\’akari da yadda abin yake a lokutan baya.
Ana samun babban sa wanda ya koshi a kan kudi naira dubu dari da hansin zuwa dubu dari da saba\’in yayin da ak samu matsakai ta kan kudu naira dubu tamanin zuwa dubu dari da ashirin.
Haka kuma farashin raguna ya kama daga dubu ashirin zuwa dubu talatin da biyar yayin da ake samun manyan raguna kan kudi naira subu sittin zuwa dubu tamanin,inda kuma farashin awaki ya fara daga naira dubu goma sha biyar zuwa subu ashirin.
Bugu da kari, kaji da zabi ana samun su kan kudi naira dubu daya zuwa dubu daya da dari biyar kana ana samun talo-talo kan kudi naira dubu biyu zuwa dubu biyu da dari uku.
Sarkin fawar Badume Alhaji Danfulani ya bayyana cewa duk da irin matsin tattalin arziki da ake fama dashi a kasa, mutane suna kokari sayen dabbobi da kaji da sauran abubuwan shagulgulan babbar sallah kamar yadda aka saba

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here