Dalilin Da Ya Sa \’Yan Nijeriya Sake Zaben Buhari – Shehu Sani

0
772
Sanata Shehu Sani A Gidan Nakasassu
Mustapha Imrana Abdullahi Daga Kaduna
DAN MAJALISAR Dattawa mai wakiltar tsakiyar Kaduna Sanata Shehu Sani, ya bayyana dalilan da za su sa Yan Nijeriya su sake zaben Buhari da kuma jam\’iyyarsa ta APC a zaben 2019 mai zuwa.
Ya bayyana hakan ne lokacin da yake ganawa da manema labarai a gidansa Jim kadan bayan yin bikin sallah Babba tare da masu bukatun musamman a Jihar.
Sanata Shehu Sani ya shaida wa manema labarai cewa shugaban kasa Buhari ya tabbatar wa da Yan Nijeriya da duniya baki daya cewa shi mai gaskiya ne tare da rikon amana don haka ya can canci a sake zabensa karo na biyu.
\”Kamar yadda sanata Shehu Sani ya ce irin ayyukan da Buhari ya aiwatar a karkashin Gwamnatin sa, ya aiwatar da ayyukan ne domin ci gaban kasa Wanda sun fi kalubalen da za a iya fadi, kuma ana yin kokarin ganin a halin yanzu duk an magance su baki daya\”.
Ya shaida wa manema labaran cewa nasarorin da Buhari ya samu alamu ne na ci gaba sakamakon rikon gaskiya Wanda za a iya cewa alamu ne na nasarar da suka wuce kalubalen da za a iya magana a kai.
Don haka ya ci gaba da cewa shugaba Buhari ya yi koakri wajen ganin ya magance matsalar cin hanci da karbar rashawa inda masu aikata irin wannan aiki suka shiga taitayinsu wanda hakan ya taimakamatuka ta wajen samun habbakar tattalin arzikin kasa, inda hakan ya ba Nijeriya damar samun kyakkyawan suna a duk fadin duniya baki daya.
\” Nijeriya karkashin Buhari ta samu tagomashi a duniya inda ake ganin kasar da daraja a fadin duniya\”.
\”Gwamnatin Buhari ta kammala wadansu ayyuka ta kuma kirkiri wadansu sababbi, ayyukan \’yan ta\’adda sun ragu kwarai wanda ya ba kasar damar samun zaman lafiya fiye da can baya\”.
Sanata Shehu Sani ya kara da cewa Gwamnatin Buhari da jam\’iyyar APC suna kokari matukar kokarin ganin sun yi maganin matsalolin rashin aikin yi da kuma makamantansu wanda \’yan kasa su shaidu ne a kan hakan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here