Mutum Miliyan Biyu Ne Za Su Yi Aikin Hajjin Bana

0
671
Rabo Haladu Daga Kaduna
KIMANIN mutum miliyan biyu ake sa ran za su halarci kwanakin aikin hajjin bana a kusa da
cikin Makkah da ke kasar Saudiyya.
Aikin Hajjin na bana ya zo ne a daidai lokacin da kasar ke kara fadada ikonta a duniya – kuma na baya-bayan nan shi ne rikicinta da kasar Kanada- inda matashin yarima mai jiran gado ke kawo sauye-sauye na siyasa da zamanantarwa a kasar.
Muhimmancin aikin Hajji ga musulmin duniya da yawansu ya kusa mutum miliyan biyu abu ne da baya sauyawa, amma yadda kasar Saudiyya ke shirya shi na sauyawa.
Karbar bakin alhazai zuwa kasar abu ne da ke ba hukumomin daular ta Saudiyya da mahukuntanta dumbin alfahari.
Amma ba shakka gudanar da wannan muhimmin aiki mai gagarumin sarkakiya na bukatar hangen nesa matuka- shi ya sa akan sami matsaloli da suka hada da rasa rayuka da dukiyoyi a kai a kai. Kasar Saudiyya ta fadada wuraren aikin Hajjin fiye da wani lokaci a cikin tarihi.
Kuma a bana suna bayyana yadda fasaha da kimiyya ke taimakawa wajen saukaka ayyukan Hajjin.
Da misali kasar ta samar da manhajar yin tarjama daga harshen Larabci zuwa wasu
harsunan duniya da kuma na bayar da taimako ga marasa lafiya, kuma a karon farko, mahajjata za su ga mata na tukin mota a bisa titunan kasar ta Saudiyya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here