Kotu Ta Ci Tarar Hafsan Hafsoshin Sojojin Nijeriya Naira Miliyan 11

0
620
Janar na soja, Tukur Burutai
Rabo Haladu Daga Kaduna
MATASA 11 daga garin Shongom a jihar Gombe za su samu Naira miliyan 11 biyo
bayan tarar da wata kotun tarayya da ke Abuja ta yiwa hafsan hafsoshin sojojin
Nijeriya sanadiyar cin zarafin da sojoji suka yi masu.
Rahotanina nacewa wata kotun tarayyar da ke Abuja ta ci hafsan hafsoshin sojojin  Janar Tukur Buratai tarar zunzurutun kudi har Naira miliyan goma sha daya saboda cin zarafin da sojoji suka yiwa wasu matasa 11 a jihar Gombe
Mai shari’a Justice Ijeoma Ojukwu ta ce yadda sojojin Janar Buratai suka kama matasa 11 a Gombe, suka tsare su tun daga ranar 6 ga watan Yulin wannan shekarar, suka ci gaba da gana masu ukuba ba ya cikin tsarin mulki ko dokokin kasa acewar Justice Ijeoma Ojukwu ta ba da umurnin a saki matasan a kuma biya kowannensu diyar Naira miliyan daya.
Maganar ta samo asali ne lokacin da matasan suka samu gawar wani dan uwansu a gonarsu a kauyen Shongom da ke jihar Gombe. Sun dauki gawar su kai ta gida sai sojoji suka gamu da su suka kama su. Tun daga lokacin ne, 6 ga watan Yuli suka shiga azabar sojojirin

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here