JABIRU A HASSAN,Daga Kano.
GWAMNAN jihar Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje yace gwamnatinsa zata ci gaba da gudanar da aiyuka masu amfani ga al\’umar jihar ta yadda kowane bangare zai sam ribar dimokuradiyya a kowane fanni.
Ya yi wannan bayani ne yayin da yake mayar da jawabi ga maimartaba sarkin kano Malam Muhammadu Sanusi na II yayin da sarkin ya ziyarce shi a gidan gwamnati cikin wani bangare na shagulgulan bikin babbar sallah.
Gwamna Abdullahi Umar Ganduje yace gwamnatin sa tana bakin kokarin ta wajen aiwatar da aikace-aikace masu muhimmanci a fadin jihar, tareda kammala wadanda ta gada daga gwamnatocin da suka gabata ta yadda al\’amura zasu inganta.
Daga karshe, gwamnan ya godewa sarkin bisa wannan ziyara ta barka da sallah da ya kai masa tareda tawagarsa, inda kuma ya sanar da cewa gwamnati zata ci gaba da fadakar da al\’uma dangane da batun mallakar katin zabe da sarkin yayi magana a kai.
Tun da fari, sarki Muhammadu Sanusi ya yabawa gwamna Ganduje bisa yadda yake gudanar da aiyukanraya kasa a fadin jihar ta Kano ba tare da nuna kasala ba. Sannan ya hori al\’umar jihar da su tabbatar aun mallaki katin su na zabe ganin yadda zabukan shekara ta 2019 suke kara matsowa.
A karshe Malam Muhammadu Sanusi ya bukaci yan siyasa dasu rika kaucewa duk wasu abubuwa dake haddasa gaba ko rikici lokutan yakin neman zabe da kuma bayan zabuka a fadin jihar kano da kuma kasa baki daya.