Mustapha Imrana Abdullahi Daga Kaduna
SHUGABAN kasar tarayyar Nijeriya Alhaji Muhammadu Buhari, ya kai ziyarar bazata sansanin sojojin da ke aikin share kazantar masu satar jama\’a, kashe mutane tare da garkuwa da mutane a jihar Zamfara da makwabtan jihohi.
Buhari dai ya kai wannan ziyarar bazata ne a yau ranar Asabar inda ya karfafa wa sojojin da ke aiki karkashin rundunar da aka yi wa suna da sharar-daji da kuma dirar-mikiya.
Shugaba Buharin dai ya Kai ziyara bazata ne bayan ya bar filin jirgin saman tunawa da marigayi Umaru Musa \’Yar aduwa da ke atsina.
Shugaba Buhari ya jinjinawa sojojin a bisa irin kokarin da suke yi na yaki da batagarin da suke kokarin bata kasa, ya bukace su da su ci gaba da aikin kawar da bata-garin.
Indai ba za a iya tunawa jihar Zamfara ta zama wani kazamin fagen kashe-kashe tare da satar jama\’a ana neman kudin fansa lamarin da ke barazana ga harkokin noma da kuma inganta tsaron da ya yi alkawarin yi.
Kuma yana yin da zamfarar ta shiga ciki ya haifar da yin hijira jama\’a na barin garuruwansu domin tsira da rayukansu.