Burin ‘Yan Sanda Su Kashe Ni Amma Zan Nuna Musu Ko Ni Wanene Wannan Karon – Melaye

0
779
Daga  Usman Nasidi
RIGIMA tsakanin jami\’an \’yan sanda da Sanata Dino Melaye na shirin daukar sabon salo a yayin da Melaye ya ce a wannan karon ya san komai, ba za\’a layen ce masa ba.
An sha sanya rana don gudanar da shari\’arsa a jihar Kogi amma zuwa ya gagare shi Sanata mai wakiltar Kogi ta Yamma Dino Melaye ya yi zargin cewa rundunar ‘yan sandan kasar nan na wani shiri na ganin sun kawar da shi daga doron kasa.
Dino Melaye ya wallafa wannan bayanin ne a shafinsa na tiwita a jiya Litinin. Inda ya ce \”Gwamnatin jihar Kogi tare da rundunar ‘yan sanda suna son yin amfani da karfi wajen kai ni garin Lokoja domin kashe ni.\” In ji Melaye.
Idan za\’a iya tunawa dai Sanata Dino Melaye ya sha artabu da ‘yan sandan kasar nan, a inda rundunar ‘yan sandan ke zarginsa da aikata wasu laifuffukan da suka hadar da kisan kai da mallakar bindiga da kuma ta\’addanci.
Kuma ko a baya-bayan nan sai da Sanatan ya bayyana cewa masu garkuwa da mutane sun yi garkuwa da shi akan hanyar sa ta zuwa wata kotu da aka gurfanar da shi a jihar Kogi.
“Wannan shi ne karo na shida da jami\’an ‘yan sanda ke yunkuri a kaina. Suna son su kai ni Lokoja da karfin tuwo, domin su kasheni\”.
“Ni ne wadanda jami\’an tsaro sun ka kaiwa hari, suna kokarin kashe ni, wakilin gidan talabijin na AIT tare da sauran ‘yan jaridu suna wurin lokacin da abin ya faru, kuma wadanda suka shiryamin wannan tuggun za su sha mamaki domin na san komai akan al\’amarin\”.
Kawo yanzu dai rundunar ‘yan sanda ta kasa ba ta kai ga mayar da martani akan zargin da Sanata Dino Melaye ya yi ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here