Gwamnatin Kaduna Ta Saka Dokar Hana Fita Awa Ashirin Da Hudu

0
653
Gwamna Malam Nasir El-Ruffa\'i na Jihar Kaduna
Mustapha Imrana Abdullahi Daga Kaduna
GWAMNATIN Jihar Kaduna karkashin jagorancin Malam Nasiru Ahmad El- Rufa\’i ta sanar da kafa dokar hana fitar tsawon awa Ashirin da hudu a yankin Kwaru da Unguwar Yero a karamar hukumar Kaduna ta arewa.
Tun farko dai Gwamnatin Kaduna Ta kafa dokar hana walwala ne da misalin karfe Bakwai na Yamma zuwa Bakwai na safiya.
Amma sakamakon irin yadda al\’amura suka kasance a yankin na unguwar Yero da Kwaru sai aka mayar da dokar zuwa awa ashirin da hudu wato dai ba shiga ba fita a yankin, kuma wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwar da Gwamnatin ta fitar mai dauke da sa hannun mai magana da yawun GWAMNAN Jihar Mista Samuel Aruwan.
Sanarwar ta ci gaba da cewa biyo bayan irin yadda Gwamnatin ta duba yanayin tsaron ne yasa aka dauki matakin hana fita a wannan yankin Baki daya sakamakon abin da ya faru a yankin mutanen biyu.
Sanarwar ta kuma yi kira ga daukacin jama\’a da su yi biyayya ga wannan mataki na hana fita kasancewar an dauki matakan tsaro domin kawo zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here