Masoyan Buhari A Arewa Barazana Ne Ga PDP -Makarfi

    0
    668
    Shugaba Muhammadu Buhari ne yake jaddada niyyarsa ta sake tsayawa takara a 2019
    Daga Usman Nasidi
    TSOHON Gwaman Jihar Kaduna kuma tsohon shugaban riko na jam\’iyyar PDP Sanata Ahmad muhammad Makarfi ya bayyana cewa idan har ana so jam\’iyarsu ta yi nasara a zaben 2019 na shugabancin kasar, to lallai sai an maida hankali ga Arewacin kasar.
    Makarfi, wanda ke neman tsayawa takarar shugabancin kasar a jam\’iyar PDP, ya bayyana hakan a a Ado-Ekiti, bayan ganawarsa da wasu jami\’an jam\’iyar, a shirye shiryen babban taron fitar da gwani na jam\’iyar.
    Tsohon gwamnan jihar Kaduna, don haka ya bukaci masu ruwa da tsaki a jam\’iyar ta PDP da kada su dogara da kafafen sada zumunta na yanar gizo kamar yadda APC ta ke yi wajen gudanar da yakin neman zabe, yana mai cewa dole a samar da hanyoyin samun kuri\’u a Arewacin kasar.
     Ya amince da cewar har yanzu shugaban kasa Muhammadu Buhari na da \’yan a-mutun-Buhari a magoya bayansa, wadanda ko me za\’a yi ba zasu ga laifinsa ba, yana mai kira ga jam\’iyar PDP data karkata hankalinta ga yankin na Arewa.
     “Dole ne muyi aiki da tunani don ganin mun canja ra\’ayin \’yan a-mutun-Buhari da ke Arewacin kasar, don karkato da hankulansu garemu\”
    A cewarsa. Dangane da batun tsige shugaban majalisar dattijai Bukola Saraki da ya dawo jam\’iyar tasu ta PDP, Makarfi ya ce: \”Cire shugaban majalisar dattijai wani al\’amarine da ya shafi kasar, amma kada PDP ta bari wannan rikici ya karkatar da hankulanta\”
    Ya ce: \”Mun san adadin da ake bukata don tsige Saraki; APC bata da wannan adadin mutanen, bata da mafi rinjaye da zasu iya cire Saraki. Don haka, wannan kawai hanyar karkatar da hankulan jama\’a ne. Babu ta yadda za\’ayi APC ta tsige shugaban majalisar dattijai, wannan ba mai yiyuwa bane\”
     Ya yi alkawarin sauya tsarin gudanarwar ayyuka a kasar, don tabbatar da cewa Nigeria ta jera kafada-da-kafada da sauran manyan kasashe da suka ci gaba a fannoni na ci gaban kasa, kana zai cire duk wani banbanci na yare, addini don hada kan kasar baki daya.hort time.

    LEAVE A REPLY

    Please enter your comment!
    Please enter your name here