Gwamnatin Katsina Ta Sayo Kayan Ilimin Kimiya Na Naira 140

0
572

 

Mustapha Imrana Abdullahi Daga Kaduna

GWAMNATIN Jihar katsina ta bayyana cewa ta kashe naira miliyan 140 domin binkasa harkokin ilimin kimiyya da litattafan kimiyyar sadarwa a cikin wannan shekarar.

Kwamishinan ma\’aikatar ilimi Furofesa Badamasi Lawal Charanchi ne ya bayyana hakan a lokacin da ya karbi bakuncin kungiyar tsofaffin daliban kimiyyar da suka Kai Masa ziyara a ofishinsa.

Kwamishinan ya kuma yi bayanin cewa Gwamnatin Jihar Katsina karkashin Jagorancin Gwamna Aminu Bello Masari, ( Dallatun Katsina) ta shirya samar da na\’urar kwamfuta ga makarantu Goma sha Takwas karkashin hukumar kula da ilimin kimiyya da fasaha a kan kudi naira miliyan dari da Talatin da shida.

Kwamishinan ya bayyana cewa Gwamnatin Jihar karkashin ma\’aikatar ilimi ta ci gaba da tafiya da Malaman kimiyya na kwantiragi kuma wadanda aka Maye gurbinsu ma duk Malaman kimiyya ne.
Badamasi Charanchi ya ci gaba da cewa kwanan nan Gwamnatin Masari ta dauki Malamai guda dari biyar da suka kasance makaman kimiyya domin su koyar a Jihar.
Tun da farko shugaban kungiyar da suka Kai wa kwamishinan ziyara Malam Mustapha Lawal ya shaidawa kwamishinan game da wasu daga cikin ayyukan da kungiyar ta aiwatar da suka hadar da bayar da shawara a makarantun sakandare, shirya taron horar da matasa tare da yi masu gargadin hannunka mai sanda game da irin hadarin da ke tattare da batun mu\’amala da miyagun kwayoyi, suna kuma shirya tarukan horarwa ga daliban da za su kammala sakandare da dai sauran su.

 

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here