Jam\’iyyar APC Ne Za Ta Ci Zaben Fitar Da Gwani Na Yan Takara

  0
  541
  Shugaba Muhammadu Buhari ne yake jaddada niyyarsa ta sake tsayawa takara a 2019

   

  Mustapha Imarana Abdullahi

  JAM\’IYYAR APC Ta bayyana cewa za ta yi zaben Kai tsaye ne domin fitar da Yan takarar da za su tsaya a karkashin ta, sabanin irin yadda ake ta yada kabarin cewa sun yanke hukuncin yin zaben daliget in ban da na shugaban kasa.

  Gwamnan Jihar Filato Barista Simon Bako Lalong Wanda shi ne ya zanta da manema labarai a ranar Alhamis da ta gabata a karshen babban taron masu ruwa da tsaki na Jam\’iyyar ya ce taron ya amince da ayi zaben daliget a dukkan zaben Yan majalisun Jihohi da na tarayya da kuma zaben Gwamna, in Banda na shugaban kasa kawai.

  Amma sai ga wata sanarwar da ta ci karo da inda mai rikon mukamin sakataren yada labarai mai magana da yawun jam\’iyyar APC na kasa Yekini Nabena, ya ce babban taron jam\’iyyar na kasa ya amince cewa ayi zaben fitar da Yan takara Kai tsaye kuma taron ya amince da kowa ce jiha ta yi zaben daliget idan sun yi taron masu ruwa da tsaki na Jam\’iyyar a matakin Jiha sun iya yin zaben idan an cimma yarjejeniyar ayi hakan.
  Su dai yayan jam\’iyyar APC musamman Talakawa na fadin cewar sun fi son ayi mutum bayan mutum ko Kato bayan Kato wato Hajiya bayan Hajiya domin hakan ne zai ba su damar zaben abin da suke so domin ya shugabance su a Kowane mataki.

   

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here