Sayar Da Kuri\’a Babbar Matsala Ce A Siyasar Najeriya – Muryar Talaka

0
588

 

Isah Ahmed, Jos

BABBAN sakataren kungiyar Muryar Talaka ta kasa a Nijeriya, Kwamared Bashir Dauda Sabo Unguwa Katsina ya bayyana cewa siyasar sayen kuru’u babbar matsala ce a siyasar Nijeriya. Kwamared Bashir Dauda ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi, a wajen kaddamar da gangamin yaki da siyasar sayar da kuru’u a zabubbukan Nijeriya da kungiyar ta gudanar a garin Jos babban birnin jihar Filato.
Ya ce sun zo garin Jos ne don kaddamar da yekuwar fadakar da jama’a kan matsalar saye kuru’un talakawa da ‘yan siyasa ‘yan jari hujja suke yi a Nijeriya.
Ya ce wannan wata matsala ce da ‘yan siyasa ‘yan jari hujja suka zaba kuma suke amfana da ita. Don haka dole ne kungiyoyin farar hula kamar wannan kungiya ta Muryar Talaka su dauki matakai, na yakar wannan mummunar dabi’a.
Kwamared Bashir ya yi bayanin cewa yanzu ‘yan siyasa sun haukace wajen neman kudade a Nijeriya, don tsayawa takara wasu gwamnonin sun ki yiwa al’ummominsu aiki, don tara kudaden da zasu yi yakin neman zabe da su a zaben shekara ta 2019.
‘’A kullum wannan matsala siyasar kudi da sayen kuru’u tana kara kazanta ne a Nijeriya. Saboda ba a hukumta wadanda suke aikata wannan laifi a Nijeriya. Misali zaben da aka yi a jihar Ekiti, an zargin sayar da kuru’a har naira dubu 3, haka a zabubbukan cike gurbi da aka gudanar a wasu jihohin Nijeriya kwanakin baya, duk an yi zargin cewa an sayi kuru’un jama’a. Tun da muka dawo mulkin damakaraxiya har ya zuwa wannan lokaci, ba a taba cewa ga wani dan siyasa da aka kama yana sayen kuru’u aka kai shi kotu aka hukumta shi ba’’.
Ya yi kira ga kungiyoyin da suka halarci wajen wannan taro zasu je su shirya irin wadannan tarurruka a kananan hukumomi da mazabu da sauran unguwanni na jihar Filato. Don a fadakar da jama’a cewa sayar da kuru’u ba zai taba samar da shugabanni na gari a Nijeriya ba.

Shi dai wannan taron gangami ya sami halartar ‘yan kungiyar Rundunar Adalci reshen jihar Filato da qungiyar zabi sonka ta kasa reshen jihar Filato, da wasu dattawan jihar da sauran jama’a daga sassa daban daban na jihar.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here