Yan Kwankwasiya Sama Da Dubu Goma Sun Koma Jam\’iyyar APC

  0
  636
  Shugaba Muhammadu Buhari ne yake jaddada niyyarsa ta sake tsayawa takara a 2019

   

  Mustapha Imrana Abdullahi

  A WANI babban taron karbar yayan Kwankwasiyya Sama da dubu Goma da suka canza sheka zuwa Gandujiyya sun tabbatar wa duniya cewa sun dauki wannan matakin ne sakamakon rashin alkiblar da suka ce sun ga kwankwaso ya kasa gane wa.

  Su dai dubban mutanen sun bayyana cewa sun canza shekar ne saboda sun Gamsu da ayyukan Gwamna Abdullahi Umar Ganduje yake aiwatar wa domin ciyar da kasar gaba.
  An dai karbi wadannan mutanen ne da suka fito daga bangarori biyu na Kwankwasiyya a Daidaita Sahu da suke sana\’ar haya da Babur na a Daidaita Sahu su sama da dubu shida.
  Sai kuma masu amfani da jar hula da ke cikin jam\’iyyar PDP suma suka canza sheka zuwa APC duk sun ce sun Gamsu da mulkin Dakta Abdullahi Umar Ganduje shi yasa suka koma Bangarensa domin samun tsira.
  Su dai wadannan mutane sun yi hidimar Kona jar hula a lunguna da sakunan Jihar Kano a kokarinsu na nuna cewa sun gaji da tafiyar Kwankwasiyya.
  An dai yi wannan babban taron karbar wadannan mutane ne a lokacin da Jagoran Kwankwasiyya Alhaji Rabi\’u Musa Kwankwaso yake taron nuna wa duniya cewa zai tsaya takarar shugabancin Nijeriya karkashin PDP a garin Abuja.
  Wadanda suka halarci wannan taron na karbar mutane. Kwankwaso da suka canza sheka sun hada da kwamishinan yada labarai Honarabul Muhammad Garba sai kwamishinan ma aikatar kananan hukumomin Jihar Kano da dai sauran manyan jagororin Gwamnatin Jihar Kano karkashin Ganduje.
  Inda Muhammad Garba ya bayyana cewa Gwamnatin Ganduje tayi matukar kokari wajen inganta tattalin arzikin Jihar da kuma ciyar da Jihar gaba a dukkan fannoni.

   

   

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here