Zaben Deliget Ne Alheri Ga APC Da Jihar Kaduna – MS Ustaz

  0
  608
  Shugaba Muhammadu Buhari ne yake jaddada niyyarsa ta sake tsayawa takara a 2019

   

  Mustapha IMRANA Abdullahi Daga Kaduna

  An bayyana tsarin fitar da Yan takara a jam\’iyyar APC na deliget a matsayin tsari Mafi ingancin da zai haifarwa APC cikakken zaman lafiya da kaunar Juna tare da Kai Kaduna ga Tudun muntsira

  Bayanin hakan ya fito ne daga bakin wani babban jigo a jam\’iyyar APC a Jihar kaduna, kuma tsohon Dan tankarar kujerar karamar hukumar kaduna ta kudu, Hon. Muhammad Sani Abdulmajid, wanda aka fi sani da MS Ustaz, a yayin da yake zantawa da manema labarai a ofishinsa da ke kaduna.

  Jigo a jam\’iyyar APC, ya kuma kara da bayyana cewa, mafi yawa daga cikin \’ya\’yan jam\’iyyar APC na jihar kaduna, ba su da sabon rajistar jam\’iyyar APC, sannan da yawa daga cikinsu katin jam\’iyyarsu ya bace, sannan ita kanta jam\’iyyar ba tada sabon rijista. A cewarsa duk wannan na daga cikin babban kalubalen da ke tattare da kalubale.

  MS Ustaz ya qara da bayyana cewa, idan akayi la\’akari da yadda jam\’iyyar APC ta gudanar da zaben fitar da gwani a zabukan shugabannin kananan hukumomi da kansiloli, tabbas za a gane cewa, akwai babban kalubale na matsalar tsaro, wanda idan akace za a kwatanta kara abin da ya faru a baya, to tabbas za a sami babban matsalar gaske.

  Dangane da haka ne, Ms Ustaz ya shawarci uwar jam\’iyyar APC ta kasa karkashin jagorancin Kwamared Adams Oshiomhole, da cewa su canja tunanin akan tsarin yin zaben mutum bayan mutum, domin akwai babban hatsari dangane da hakan. A cewar MS Ustaz

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here