Uwar Jam\’iyyar PDP Ta Sake Rushe Kwamitin Riko Na Jihar Kano

  0
  625

  Daga Usman Nasidi

   

  Uwar jam’iyyar PDP ta kasa ta sake rushe kwamitin riko da ta kafa a jihar Kano don sake fadada shi domin ya kunshi kowanne bangare na magoya bayan tsofin gwamnonin jihar; Rabi’u Musa Kwankwaso da Ibrahim Shekarau.

  A ranar Talata, ne wani hadimin, Ibrahim Shekarau, tsohon gwamnan jihar Kano, ya bayyana cewar Shekarau din ya koma APC kafin daga bisani tsohon gwamnan ya musanta hakan.

  Sakataren yada labaran jam’iyyar PDP, Kola Ologbondiyan, ya shaiadawa cewar Shekarau bai fita daga jam’iyyar PDP ba domin bai aiko masu a rubuce ba.

  Shugaban jam\’iyyar PDP na kasa; Uche Secondus Ya ce jam’iyyar ta tuntubi tsohon gwamnan a jiya kuma ya tabbatar masu cewar har yanzu yana jam’iyyar PDP.

  Ologbondian ya kara da cewar jam’iyyar PDP a shirye take ta saurari korafi ko wata shawara da duk wani mamba a jam’iyyar zai bayar muddin domin zasu haifar da sulhu da zaman lafiya.

  Shugabancin jam’iyyar ya tabbatar da cewar ba zasu taba yin shakulacin bangaro da korafin ‘ya’yanta a jihar ta Kano ba.

  Kazalika ta bawa dukkan ‘ya’yanta a jihar ta Kano tabbacin cewar zata yi tafiya da kowa domin ganin an gudu tare an tsira tare.

   

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here