Daga Usman Nasidi
WATA kungiya mai wayar da kan jama\’a, Enough is Enough (EiE) Nigeria, ta shigar da kara a babban kotun Abuja inda ta ke bukatar kotu da kori dukkan \’yan majalisa da suka sauya sheka domin a gudanar da zabin maye gurabensu.
Wasu daga cikin \’yan majalisan da suka sauya sheka sun hada da shugaban majalisa Bukola Saraki da tsohon shugaban marasa rinjaye, Godswill Akpabio.
A yayin da Saraki ya sauya sheka daga APC zuwa PDP, Akpabio ya yi kishiyar hakan. Kungiyoyi sun hada kai don kai Saraki da Akpabio kara kan sauyin sheka.
A karar da kungiyar ta shigar mai lamaba FHC/ABJ/CS/923/2018 a ranar 28 ga watan Augustan 2018, kungiyar ta ce \’yan majalisar sun fice daga jam\’iyyun da suka basu inuwar takara kuma su kayi nasara ba tare da rabuwan kai a jam\’iyyar ba.
Kungiyar ta ce dan majalisa yana iya cigaba da kasancewa a kujerarsa ne bayan sauya sheka idan jam\’iyyarsa ta rabu kashi biyu kamar yadda ta faru a shari\’ar Abegunde da majalisar jihar Ondo a 2015.
Kungiyar kuma ta bayar da misalin abinda ya faru a majalisar jihar Kaduna inda Kakakin majalisar ya sanar da cewa za\’a gudanar da zaben maye gurbin wasu \’yan majalisa biyu da suka sauya sheka.
\”Muna son a cigaba da daukan irin wannan matakin a dukkan jihohin Najeriya da babban birnin tarayya.
A halin yanzu ba\’a tsayar da ranar sauraron karar ba saboda ba\’a mika shari\’ar ga alkalin da zai saurare ta ba.
Shugaban tsare-tsare na kungiyar, Dapo Awobekun ya bukaci a kotun tayi gagawar fara sauraron shari\’ar.