Za A Daina Bawa Daluban Firamare Abinci A Takarda a Jihar Kano

0
677
Shugaba Muhammadu Buhari

 

Rabo Haladu Daga Kaduna

GWMNATIN tarayya za ta dauki matakan
gyara a shirinta na ciyar da daliban
Firamare a fadin kasarnan .

Yayin da makonni kadan suka rage daliban
makarantun sakandare da Firamare su koma makaranta bayan kammala hutun shekara,

Mai baiwa shugaban ‘kasa shawara kan harkokin yaki da fatara tsakanin ‘yan kasa ta ce zasu dauki matakan gyara dangane da batun zubawa dalibai abinci akan takarda karkashin tsarin ciyarwa na gwamnatin tarayya wadda ofishinta ke aiwatarwa.

Wakilinmu daya zagaya wasu makarantu dake cin gajiyar shirin a Kano, ya ga yadda daliban dake cin abinci akan takarda.

Sai dai a zantawa da wakilin namu yayi a Kano ya danganta laifin akan gwamnatin jihar Kano. yana mai cewa gwamnatin jiha
ce ya kamata ta samarwa da daliban kwanikan da za a rinka zuba musu abinci, domin kudin da gwamnatin tarayya take bayarwa na abinci ne.

Kamar yadda aka shirya wannan tsari na ciyar da dalibai, shine gwamnatin tarayya zata biya masu dafa abinci kudadensu a hannunsu ba tare da an baiwa wani ya basu ba.
Maganar kwanikan da za a rika zuba musu abinci ya rage ga gwamnatin jiha, idan
itama ba za ta iya bayarwa ba, to ta nemi daliban su rinka zuwa da kwanan abincinsu daga gida.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here