Daga Usman Nasidi
A kokarin sa na ganin cewa an yi adalci a rabon mukaman gwamnati, ba tare da nuna wariyar jinsi ba, Gwamnan jihar Benue Samuel Ortom ya nada uwargida Veronica Onyeke, a matsayin sabuwar shugabar ma\’aikatan jihar.
Biyo bayan wannan sanarwa ta nadin Onyeke, hakan yasa ta zamo mace ta farko da gwamnatin jihar ta taba nadawa a matsayin shugabar ma\’aikatan jihar.
An haifi uwargida Veronica a karamar hukumar Ogbadibo da ke a jihar, kafin bata mukamin shugabar ma\’aikatan jihar, ita ce babbar sakatariya a ofishin mataimakin gwamnan jihar.
Gwamnan, a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun sakataren watsa labaransa, Terver Akase, ya yi nuni da cewar sabuwar HOS zata maye gurbin Injiniya George Ede wanda yake shirin yin ritaya.
A yanzu, Onyeke ta dauki kambu na zamowa mace ta farko da aka baiwa mukamin shugabancin ma\’aikatan jihar, tun bayan shekaru 42 da kafuwar jihar.
Majiyarmu ta samu labarin cewa a ranar asabar data gabata ne akalla ma\’aikatan jihar Benue 4,000 ne suka zana jarabawar karin matsayi a Makurdi, babban birnin jiahr.
Babban Sakatare a ma\’aikatar \’Bureau of Establishment\’, mista Ode Echele, ya bayyana hakan ga manema labarai a Makurdi. Echele ya ce ma\’aikatan da suka zauna jarabawar a ranar asabar, 27 ga watan Augusta, suna a matakin aiki na 6 da wadanda ke sama da hakan.