Buhari Ya Roki Yan Najeriya Dake Kasashen Waje Dasu Dawo Najeriya

0
541

 

Daga Usman Nasidi

SHUGABAN kasa Muhammadu Buhari yayi kira gay an Najeriya mazauna kasashen waje dasu dawo gida Najeriya don a taru a ciyar da kasar gaba, saboda a cewarsa Najeriya ta fara gyaruwa, inji rahoton jaridar Daily Trust.

Majiyarmu ta samu labarin cewa ministan kimiyya da fasaha, Ogbonnaya Onu ne ya bayyana haka a yayin ganawa da yan Najeriya mazauna kasar Amurka, inda yace a yanzu sabuwar Najeriya ake ginawa a karkashin shugabancin Muhammadu Buhari.

Ministan ya tafi kasar Amurka ne don ya wayar ma yan Najeriya mazauna kasashen waje kai dangane da sabuwar dokar da shugaba Buhari ya rattafa ma hannu a kwanakin baya wanda ta nemi a fara duba yan Najeriya kafin wata kasa game da batun daukan aiki ko bada kwangila, musamman a fannin kimiyya, kirkire kirkire da kuma fasaha.

Ministan ya jinjina ma mazauna kasashen waje dangane da kudaden da suke aikawa Najeriya, wanda ya kai dala biliyan 22 a duk shekara, inda yace hakan na matukar taimaka ma tattalin arzikin Najeriya.

“Amma mun fi son ku dawo Najeriya, komawarku Najeriya nada matukar amfani garemu, mun san ba kowa bane zai iya dawowa gida, amma koda kadan kadan ne ku fara dawowa. Sakon dana zo muku dashi shine abubuwa sun fara gyaruwa a kasarnan.

“Gaskiyar maganar itace babu yadda za’ayi ka gyara matsalolin baya farat daya, amma abu mai muhimmanci shine an fara samun canji, ba wai zamu yi ta jira bane har sai komai ya gyaru a Najeriya sa’annan zamu dawo.” Inji shi.

Bugu da kari Ministan ya bayyana musu cewa Naejriya bata samun gagarumin cigaba ta bangaren manyan ayyuka ba kamar a wannan gwamnatin, inda yake akwai aikin gina manyan hanyoyi da sauransu dake tafiya a duk fadin kasarnan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here