Gwamnati Tayi Watsi Da Masu Kiwon Kaji-Abdulrahman Lawal

  0
  766

   

   Isah Ahmed, Jos

   

  WANI  fitatcen mai kiwon kaji a jihohin Bauchi da Filato kuma mai gonar kiwon kajin nan, ta Yankari Farms dake karamar hukumar Toro a jihar Bauchi Alhaji Abdulrahman Lawal ya bayyana cewa duk da kokarin da wannan gwamnati take yi, na bunkasa harkokin noma a kasar nan. Ta hanyar tallafawa manoman kayayyakin amfanin gona, na bangarori daban daban, amma tayi watsi da masu kiwon kaji. Alhaji Abdulrahman Lawal ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu.

  Ya ce wallahi mu masu kiwon kaji gwamnati bata shirya mana komai na tallafi ba, a cikin wannan tafiya da ake yi, na tallafawa manoman kasar nan.

  Alhaji Abdulrahman ya yi bayanin cewa ana  ta kiran kowa a bangarorin manoma  ana basu  tallafin  injinan ban ruwa da taki da magunguna  feshi da kuxaxe. Amma ba a kula da masu kiwon kaji ba.

  Har’ila yau ya ce ka dubi lokacin da muka yi asara a annobar murar tsuntsaye da aka yi a kasar nan, sai da muka yi shekaru uku, ba a bamu tallafin ko kwabo ba.

  Ya ce masu gidajen kaji da dama sun rufe gonakinsu, saboda mawuyacin halin da  suka shiga  a kasar nan, sakamakon  rashin tallafin da ake yiwa masu. Don haka yanzu kiwon kaji ya yi baya a kasar nan.

  Ya ce taimakawar da harkokin kiwon kaji  yake yi wajen bunkasa harkokin noma a kasar nan yana da yawa.

  ‘’Yau masarar da ake nomawa a Nijeriya idan ba dan masu kiwon kaji ba, sai dai aje a zubar da ita, domin  kashi 95 na masu zuwa kasuwannin kasar nan, suna sayen masara, masu kiwon kaji ne. Don haka masu gidajen kaji ne suke cin masara da waken soya da quli qulin da ake yi a qasar nan. Baya ga kashin kajin da muke fitarwa wanda manoma suke amfani da shi wajen gudanar da harkokin nomansu’’.

  Alhaji Abdulrahman ya ce yanzu idan aka ce babu kwai a Nijeriya, wanne irin hali  ne za a shiga?. Sannan ga  wadanda suke sayen kwan nan suna tafiya da shi lungu lungu na kasar nan. Baya ga ma’aikatan da masu gidajen kajin suke dauka aiki.

  Ya ce tallafi na farko da za a yiwa masu kiwon kaji a kasar nan shi ne ayi masu inshora ta gaskiya, wanda za a rika biyan su, idan wata asara ta taso masu.  Bayan haka gwamnati ta rika sayen masara a wajen manoma tana sayar masu kan farashi mai rahusa, don su ji dadin gudanar da wannan sana’a  cikin sauki.

   

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here