Isah Ahmed, Jos
WANI jigo a jam’iyyar APC kuma shugaban kungiyar dillalan mota ta Nijeriya reshen jihar Filato Alhaji Yahaya Muhammad Kega, ya bayyana cewa yawaicin manyan ‘yan siyasar da suka fice daga jam’iyyar APC suka koma jam’iyyar PDP siyasarsu tazo karshe a Nijeriya. Alhaji Yahaya Muhammad Kega ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu a garin Jos, babban birnin jihar Filato.
Ya ce wadanda suka canza sheka daga jam’iyyar APC suka kuma jam’iyyar PDP, dama haka rayuwar siyasarsu take a Nijeriya. Kuma mutane ne da basu da alkibla, wadanda damuwarsu ce take gabansu, ba damuwar ‘yan Nijeriya ba. Kuma su dai bukatarsu kullum ya kasance ana yi dasu.
Alhaji Yahaya Kega ya yi bayanin cewa ai dama wadannan mutane a PDP suke, kafin su canza sheka su dawo jam’iyyar APC su ci zabe, bayan da suka ci zaven suka ci amana. Ya ce ganin cewa yanzu ga an gano su, ba zasu sake samun damar tsayawa zabe a APC ba, shi ne suka canza sheka zuwa PDP. Wato suka koma inda suka fito.
Ya ce babu shakka zuwan gwamnatin shugaba Buhari ta budewa ‘yan Nijeriya ido, saboda adalcin da gwamnatin tazo da shi, su kuma irin wadannan mutane basa son wannan adalci da gwamnatin Buhari tazo da shi.
Alhaji Yahaya Kega ya yi kira ga talakawan Nijeriya su yi amfani da wannan dama da suka samu, su zabi mutanen kirki wadanda zasu taimakawa gwamnatin Buhari a zaben badi mai zuwa.
Da ya juya ga tsarin zaben tsayar da ‘yan takara da jam’iyyar APC ta fitar kuwa, ya ce gaskiya shi a ra’ayinsa ayi zaben ‘yar tinke a dukkan kujerun takarar da za a zaba, kamar yadda shugaban kasa Muhammad Buhari ya ce ayi a zaben tsayar da dan takarar shugaban kasa.
‘’Domin wannan zabe shi ne zaben adalci, wato Jama’a ‘yan jam’iyyar APC su fito tun daga mazabu zuwa kananan hukumomi da jihohi su zabi ‘yan takarar da suke so. Irin wannan zabe shi ne zai fitar da ainihin ‘yan takara nagari’’.