Zaben Yar Tinke Ne Mafita A APC

  0
  644

   

  Mustapha Imrana Abdullahi Daga Kaduna

  SANATA mai wakiltar mazabar Kaduna ta tsakiya da kuma tsohon sanata Muhammadu Sani Sale sun bayyana matsayinsu game da batun zaben fitar da Yan takara a Kowane irin mataki a Jam\’iyyar APC inda suka ce ba su amince da zaben deliget ba.

  Sun dai bayyana hakan ne a wajen taron manema labarai da suka yi a cibiyar Yan jarida da ke Kaduna

  Sun tabbatar da matsayinsu da cewa su a matsayinsu za su amince ne kawai da aiwatar da zaben fitar da Yan takara irin na Yar tinke ko Kato bayan Kato, hajiya bayan Hajiya da ake cewa Malam bayan Malam ko malama bayan malama, amma a tsarin su ba su amince da zaben deliget ba Kuma sun aikewa uwar jam\’iyyar APC ta kasa irin matsayinsu.

  \”Mu muna kokarin kawo wa APC mafita ne saboda akwai wadansu jam\’iyyun da za a shiga zabe tare da su kuma su sauran kansu a hade yake don haka dole a tabbatar da an aiwatar da abin da mutane ke bukata domin a samu mafita a zaben gama Gari\”.

  Duk kansu sun ce an gayyace su ofishin Jam\’iyyar APC na Jihar Kaduna sun Kuma Je amma ba a bari kowa ya bayyana abin da ke bakinsa ba, don haka abin da aka cimmawa ra\’ayi ne kawai na wadansu mutane a wani bangare

  \”Shi yasa muke bayani mu biyun nan tare da sauran Yan takarar da ba su amince da irin wannan zaben fitar da Yan takarar Kai tsaye ba, mun Kuma rubuta matsayarmu ga uwar jam\’iyyar ta kasa\”.

  Sun ci gaba da bayanin cewa mafita dai shi ne ayi abin da jama\’a ke bukata domin a samu nasara a zaben gama Gari kasancewa mutanen da za a shiga zaben nan da su sauran kansu a hade yake, saboda haka me zai sa jam\’iyyar APC Za ta kasa yin abin da ya dace?

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here