Mustapha Imrana Abdullahi
Shugaban Jam\’iyyar APC na kasa Kwamared Adam Oshiomhole, ya jagoranci wata karkarfar Tawagar masu fada a ji inda suka ziyarci tsohon Gwamnan Kano Malam Ibrahim Shekarau a Kano.
Shugaban APC da wasu mambobin Jam\’iyyar sun Isa Fadar Mundubawa ne wato gidan Malam Ibrahim Shekarau Sardaunan Kano domin yi Masa maraba da shiga jam\’iyyar APC koda yake shi yana daga cikin mutanen da suka kirkire ta.
Daga cikin mahalarta wannan taron maraba har da Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje tare da rakiyar dimbin magoya bayansa suna ta fadin \”APC\”.
Shekarau dai ya bar PDP ne a cikin satin nan ya kuma koma APC da magoya bayansa.
A bayaninsa da ya rubuta a kan shafinsa na Tuwita mai magana da yawun APC na kasa Yekini Nabena ya rubuta cewa idan taron Gizo Gizo suka hada Kai za su iya dabai Baye Zaki su kuma daure shi tamau\”.
Shekarau Ya bayyana Komawarsa APC bayan wani taron irri tare da shugaba,Gwamnan Kano da kuma masu fada a ji na Jam\’iyyar APC.