Dan Takarar Gwamnan Jihar Kaduna Jalal Falal Ya Gargadi APC

  0
  584
  Mustapha Imrana Abdullahi Daga Kaduna

  Dan takarar neman kujerar Gwamnan Jihar Kaduna Sa Jalal Falal ya Gargadi Jam\’iyyar APC musamman reshen Jihar Kaduna game da yin zaben karfa karfa ko Nadin duk wani Dan takara ta hanyar da ta sabawa kundin tsarin mulkin APC.
  Sa Jalal Falal dai ya bayyana hakan ne lokacin da yake tattaunawa da manema labarai a cibiyar Yan jarida da ke Kaduna
  Jalal Falal, ya ci gaba da cewa hakika ba tsarin APC bane yin nadi ko karfa karfa musamman wajen batun tsayar da Yan takara.
  \”Mu muna fadi da babbar murya cewa bama son yin zaben deliget a lokacin fitar da Yan takara don haka muke yin cikakken bayanin cewa ayi zaben Kato bayan Kato, hajiya bayan Hajiya ko Alhaji Bayan Alhaji domin yin irin wannan zabe shi ne mafita ga APC\”.
  Kamar yadda ya ce APC ta yi wa jama\’ar kasa alkawari don haka ya dace a tsaya a kan alkawuran da aka yi wa jama\’a.
  Ina kira ga Jam\’iyyar APC reshen Jihar Kaduna da ta yi koyi da uwar jam\’iyyar ta kasa da kuma tsarin da shugaban kasa ya zaba za\’a yi a lokacin zaben fitar da Dan takara na shugaban kasa Wanda yake shi ne kato bayan Kato amma ba kamar yadda APC reshen Kaduna ta fitar da sanarwa ba, na zaben deliget hakika bamu Goyon bayan zaben deliget ko Kadan.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here