Mustapha Imrana Abdullahi
Sanatan da ke wakiltar Kaduna ta tsakiya kwamared Shehu Sani a ranar Asabar 8 ga watan Satumba 2018 ya samu nasarar Mamaye sakatariyar jam\’iyyar APC tare da tururuwar magoya bayansa daga kananan hukumomin da yake wakilta Bakwai da suka fito duk a cikin Jihar Kaduna amma suka same shi a Abuja babban birnin tarayyar Nijeriya.
Dumbin magoya bayan sun yi tururuwa zuwa hedikwatar APC ne ta kasa domin shaida sayen Fom din da Gwarzon nasu yadda ya Sayi Fom din da zai sake tsayawa takara a shekarar 2019 mai zuwa.
Da yake yi wa magoya bayan nasa jawabi ya gaya wa dimbin magoya bayan cewa yana umartarsu ta hanyar neman Alfarma su da su kara Shirin aiwatar da aikin da suka yi a lokutan zabe na zaben jam\’iyyar APC a shekarar 2019 mai zuwa.
Magoya bayan sun rika daga murya da karfi suna cewa mu zaben Kato bayan Kato muke so.
Shi kuma Sanatan ya tabbatar masu cewa \”ba zamu Baku kunya ba kamar yadda kuka Sani\”.
Kasancewar sanata shehu Sani a sakatariyar jam\’iyyar duk ya dusashe sauran Yan takarar da ke wajen da suma suka Je domin sayen Fom, musamman wadanda suka zo daga wurare masu nisa irin su Jihohin Kogi da Enugu.