Rashin Adalci Ya Sanya Na Janye Daga Takara – Sa Jalal Falal

  0
  608

  Mustapha Imrana Abdullahi Daga Kaduna

  Dan takarar Gwamnan Jihar Kaduna karkashin jam\’iyyar APC Matashi Sa Jalal Falal ya bayyana wa manema labarai a Kaduna cewa ya Janye Daga takarar ne saboda irin rashin gaskiyar da suka ga an shirya aiwatarwa a lokacin zaben fitar da dan takarar jam\’iyyar.
  Ya tabbatar wa manema labarai hakan ne a garin Kaduna cewa akwai matsala a batun zaben fitar da Yan takarar da aka shirya yi a Jihar karkashin APC.
  \”Mun yi zaton cewa abin da aka shirya yi na son zuciya a zaben fitar da Yan takara karkashin APC za\’a gyara lamarin amma sai ga shi lamarin ya kara tabarbarewa fiye da can baya, domin kuwa ana Cire sunayen wasu ana ta Maye gurbinsu da wadanda wani ke bukatar ayi Masa hakan\”.
  Ta yaya za a rika zama a cikin wani daki ana rubuta sunayen mutanen da ake bukata da nufin su za su yi zabe a lokacin zaben fitar da Yan takara karkashin APC?
  Ya kara da cewa sun tabbatar da cewa ba za a yi wa jama\’a adalci ba, \” mun yi taro da tuntubar bangarorin jama\’a daban daban da suka hadar da Yan kasuwa, Yan kungiyoyi da makamantansu mun Kuma gaya masu halin da ake ciki an dauki mataki kamar yadda muka gaya maku don haka muna godiya da irin yadda suke bamu hadin Kai da Goyon baya\”.
  \” Babu adalci a tsarin da jam\’iyyar APC da sa hannun Gwamnatin Kaduna suka aiwatar kuma da hakan ake Shirin yin zaben fitar da Yan takara a Jihar kaduna, don haka bamu ba wannan tsarin\”. Inji Jalal Falal.æ

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here