Sarkin Gumel Ya Yabama Kamfanin Bizi Mobile Da Bankin Jaiz

0
875
Mustapha Imrana Abdullahi Daga Kaduna
Mai Martaba Sarkin Gumel, Alhaji Ahmed Muhammad Sani, ya bayyana matuqar farin cikinsa dangane da yadda Bankin Jaiz, ya Kulla yarjejeniyar agency banking da kamfanin Bizi mobile Cashless consultant limited, wato ya sahalema kamfanin bizi mobile da ya yi mu\’amula ta kudade kai tsaye da Al\’umma a madadin bankin jaiz, wanda a sanadiyar hakan ne, har Bankin na Jaiz ya qudiri aniyar bude rassan bankinsa domin hada hadar kasuwanci a Karamar hukumar Gumel da ke Jihar Jigawa.
Sarkin Gumel ya bayyana haka ne a yayin da ya karbi tawagar shugabannin Bankin Jaiz a fadarsa da ke Gumel, a yayin da suka kawo masa ziyarar ban girma, da kuma bayyana masa ci gaban da suka samu na qulla yarjejeniya da kamfanin bizi mobile domin  ganin sun inganta rayuwar Al\’ummar Garin Gumel, ta hanyar hada hadar kudade irin na zamani, wato agency banking.
Sarkin na Gumel ya ci gaba da bayyana cewa, \”Ina matukar godiya ga \’Danmu, \’Dan wannan masarauta, Alhaji Aminu Bizi, bisa ga irin kishin Al\’ummarsa da yake da shi a ko da yaushe, domin duk fadin Garin Gumel, babu wanda ya taba tunanin ya kawo mana banki domin ci gaban mutanenmu sai Aminu Bizi. Tabbas wannan abin a yaba masa ne, domin ya nuna mana cewa shi \’Da ne na kwarai \’Dan albarka, kuma Insha Allah zai gama da duniya lafiya.\”
Daga karshe Sarkin na Gumel, Alhaji Ahmed Muhammad Sani, ya gode ma Bankin Jaiz, a bisa yadda suka zabi suyi mu\’amula da kamfanin bizi mobile. A cewarsa, a shirye Masarautar Gumel take domin bayar da duk wata gudunmuwa da ake bukata, idan bukatar hakan ta taso.
Shima a nasa jawabin, Babban Manajan Darkatan Bankin Jaiz, Malam Hassan Usman, ya bayyana ma Sarkin na Gumel cewa, shi da daukacin tawagarsa sun zo Gumel ne domin amsa gayyatar Alhaji Aminu Bizi, domim bude Babbar kasuwar Kankana ta Garin Kangarwa, sannan da kuma bikin sanya hannun takardar yarjejeniya kulla hada hadar kasuwanci ta agency banking tsakanin bankin jaiz da kamfanin bizi mobile, domin rage ma Al\’ummar kasar nan wahalhalun da suke fama da shi ta hanyar ajiyar kudade a bankuna.
Shugaban bankin jaiz, ya kara da bayyana cewa, kasancewar irin Namijin kokarin da suka ga kamfanin bizi mobile ke da shi, da kuma yawan rassa, rassa da kamfanin ke da shi, hakan ya sanya suka naimi kamfanin bizi mobile domin ganin sun kulla yarjejeniya ta agency banking, wato sun sahalema kamfanin bizi mobile, da yayi mu\’amala ta kudi kai tsaye da Al\’umma a madadin bankin jaiz.
Da yake nasa jawabin godiyar, Shugaban Rukunonin kamfanin Bizi Mobile, Alhaji Aminu Bizi, ya gode ma Mai Martaba Sarkin Gumel, a matsayin Mahaifi wanda a ko da yaushe yake kokarin ganin ci gaban \’ya\’yansa. A cewarsa, babu abin da zai ce, sai dai Allah ya ja kwanan Mai Martaba Sarkin Gumel.
Alhaji Aminu Bizi, ya bayyana ma Sarkin cewa, yau sun kulla yarjejeniya da bankin jaiz, domin ganin an rage ma Al\’umma irin wahalhalun da suke fama da shi, musamman na karancin bankuna a yankunan karkara, wanda hakan ba karamin koma baya ga Al\’umma yake janyowa ba. A cewarsa, musannan a yayin da aka biya albashi, wanda a lokacin sai an har hada katinan biyan kudi na ATM sama da guda hamsin, sannan a tura mutum daya zuwa banki birni domin ya curo, wanda a cewarsa hakan ba karamin babban hatsari ba ne.
Alhaji Aminu Bizi, ya kara da cewa, wannan da wasu dalilai ta sanya suka kulla yarjejeniya da bankin jaiz, domin ganin sun rage ma Al\’ummar kasar nan wahalhalu wajen hada hadar kudade, ta hanyar agency banking, wato ma\’ana, samar da agent daga cikin Al\’umma, batare da sun sha wahala zuwa birni domin cire kudi ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here