JABIRU A HASSAN, Daga Kano.
MANOMAN tumatur dake jihar kano sun nemi a kara kafa kamfanonin sarrafa tumatur domin bunkasa noman sa ta yadda tattalin arzikin kasa zai bunkasa ta fuskar noma rani da damina.
Wannan tsokaci ya fito ne daga wasu daga cikin shugabannin kasuwannin tumatur dake yankunan karkara a jihar kano cikin wata zantawa da suka yi da wakilin mu wanda ya ziyarci wasu daga cikin kasuwannin sayar da tumatur dake fadin jihar.
A kasuwar tumatur ta Dakatsalle, kasar tattarawa kuma yankin karamar hukumar Dawakin Tofa, Gaskiya Tafi Kwabo ta tattauna da shugaban kasuwar Malam Yahuza Dakatsalle, wanda ya bayyana cewa ko shakka babu manoman tumatur suna bukatar a samar da kamfanonin sarrafa shi rani da damina domin akwai manoman tumatur masu sumbin yawa a jihar kano.
Yace rashin samar da tsayayyen kamfanin sarrafa tumatur yasa a wasu lokutan manoman suke tafka asara wanda hakan ta sanya ya zamo dole wasu suke barin noman sa, tareda jaddada bukatar ganin an samar da kamfanonin sarrafa tumatr a kalla guda uku a jihar kano somin inganta sana-ar noman sa.
Sannan yayi amfani da wannan dama wajen yin fatan alheri ga baki mauzuwa sayen tumatur wannan kasuwa daga Legas da Warri da Abuja da Fatakwal da sauran jihohi na sassan kasarnan, inda kuma ya tabbatar da cewa kasuwar Dakatsalle zata ci gaba da karrama dukkanin masu zuwa wannan kasuwa saye ko sayar da tumatur.
A nasa bangaren, sarkin kasuwar Zaura Malam Rabi\’u maikasuwa yace samar da kamfanonin sarrafa tumatur zai taimaka wajen habaka noman sa da kuma samar da aiyukan yi a tsakanin al\’uma, sannan yayi kira ga masu iko na ciki da wajen kasarnan dasu rika kakkafa masana\’antu na sarrafa kayan amfanin gona domin inganta su maimakon a barsu su lalace.
Wani jigo a sana\’ar sayarda kayan gwari kuma daya daga cikin shugabannin kungiyar masu sana\’ar gwari ta kasa Alhaji Usman Dan Gwari ya bayyana cewa suna nan suna daukar kyawawan matakai na ganin an samar da masana\’an tu na sarrafa kayan amfanin gona musamman tumatur, inda kuma ya yabawa Alhaji Sani Dangote bisa tunanin da yayi na kafa kamfanin sarrafa tumatur a Kadawa, sai dai yayi kira ga hukumar gudanarwar kamfanin da ta farfado da harkokin kamfanin domin ya ci gaba da aki sosai.