Buhari Ya Nada Yusuf Magaji Bichi Shugaban Dss

0
584

Mustapha Imrana Abdullahi

SHUGABA Muhammadu Buhari ya amince da Nadin Yusuf Magaji Bichi, (fwc) a matsayin sabon Darakta Janar na hukumar tsaron Yan sandan farin kaya ta DSS

Kafin Nadin nasa Yusuf Magaji Bichi ya kasance mai aikin binciken kwakwaf a cikin tsananin sirri a hukumar.

Ya Halarci makarantar sakandare ta garin Dan Batta da ke Jihar Kano ya kuma halarci jami\’ar Ahmadu Bello Zariya inda ya karanci ilimin kimiyyar siyasa.

Sabon Darakta Janar din ya Fara aikin sa ne a hukumar a bangaren tsaro na ofishin sakataren Gwamnatin Jihar Kano inda ya shiga aikin tsohuwar hukumar tsaron farin kaya ta kasa (NSO) wadda a yanzu ta zama hukumar DSS.

Bichi ya samu halartar horo a kan ayyukan Tara bayanan sirri, mai kula da daukar harkokin bayanan sirri a kasar Ingila, ya kuma halarci kwalejin samar da bayanan tsaro ta kasa.

Sabon shugaban hukumar tsaron farin kayan ya shiga aikin ne da kwarewar aikin tattara bayanan sirri, aikin binciken samar da bayanai dalla dalla, aikin dai daita ma su rikici, ayyukan bincike bincike,da dai sauran bangarorin da suka hadar da tattalin al\’umma.

Bichi ya kuma yi aiki a matsayin Daraktan tsaron farin kaya a Jihohin Jigawa, Neja, Sakkwato da Abiya.

Ya Kuma yi aiki a matsayin Darakta a kwalejin horar da Jami an farin kaya ya kuma yi aikace aikace a bangarorin hukumar daban daban.

Yusuf Magaji Bichi ya dai yi aure da yaya da dama.

Duk wannan na kunshe ne cikin wata sanarwar da mai taimakawa shugaban kasa na musamman a kan harkokin yada labarai Malam Garba Shehu ya sanya wa hannu aka rabawa manema labarai a Abuja, a ranar 13 ga watan Satumba 2018.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here