Gwamnatin Kaduna Na Bukatar N70bn Domin Wani Muhimmin Aiki A Bangaren Ilimi

0
534

 

Daga Usman Nasidi

WANI kwararen mai nazarin gine-gineda ke aiki da Hukumar Kula Ilimin Frimari (SUBEB), Mr Jonathan Joseph, ya ce hukumar na bukatar a kalla N70 biliyan domin gyaran makarantun frimare na gwamnati fiye da 4,200 a jihar

Joseph ya yi wannan maganar ne a yau Litinin yayin da ya ke amsa tambayoyi daga manema labarai a wajen wani taron wayar da kan shugabanin kafafen yada labarai kan hanyoyin da za su inganta watsa ayyukan hukumar

Wata kungiya zai kai, Legal Awareness for Nigerian Women na ta shirya taron domin neman taimakon \’yan jarida wajen sanya idanu kan ayyukan da SUBEB keyi a fanin ilimi a jihar.

Joseph ya ce an cimma matsaya kan adadin kudin bayan an gudanar da bincike mai zurfi shekaru biyar da suka shude domin gano yawan kudin da ake bukata muddin ana son inganta gine-gine a dukkan makarantun frimare na gwamnati da ke jihar.

Jami\’in ya ce hukumar ta samu N2 biliyan da N2.5 biliyan duk shekara daga UBEC da kuma gwamnatin jihar Kaduna cikin shekaru uku da suka gabata sai dai wadandan kudaden ba za su wadata ayi dukkan ayyukan ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here