Isah Ahmed, Jos
SAKATAREN kungiyar manoman shinkafa ta jihar Filato, Dauda Aku ya bayyana cewa manoman shinkafa na jihar Filato mutum 5802 ne aka rabawa rancen kayayyakin aikin noman shinkafa, da suka hada da taki da irin shinkafa da injinan ban ruwa da magungunan kashe ciyawa da qwari a karqashin shirin bayar na rancen noma na Anchor Borrowers na babban bankin Nijeriya a ‘yan kwanakin nan.
Dauda Aku ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu a garin Jos, fadar gwamnatin jihar Filato.
Ya ce a wannan rance babu maganar bayar kudi, sai dai wadannan kayayyaki da aka baiwa manoman, kuma za a biya shi ne a cikin watanni 12. Wato idan manomi ya yi noman damina zai biya kashi 30, idan ya yi noman rani zai biya kashi 30, idan kuma ya sake noman damina zai biya kashi 40. Kuma da shinkafar da manomi ya noma ne, zai biya wannan rance.
Ya ce wannan aiki na bayar da rancen kayayyakin noman shinkafa da aka baiwa manoman jihar ta Filato, da babban babban bankin Nijeriya ya bayar ta hanyar bankin Unity da kungiyar manoman shinkafar. Tun da farko sai da suka bi suka yi rigistar duk wani manomin shinkafa suka karbi nambar banki ta BVN, na kowanne manomi suka dauki hoton ‘yan yatsu da lambar wayar. Kuma suka je suka gwada gonakin manoman da daukar hotinan su, daga nan aka kawo kayayyakin aka raba masu.
‘’Babu shakka wannan shiri na bayar da rancen kayayyakin aikin noman shinkafa da gwamnatin tarayya ta kirkiro abu ne mai kyau, wanda zai bunkasa noman shinkafa a Nijeriya. Ta yadda nan gaba kadan za a daina shigo da shinkafa Nijeriya daga qasashen waje’’.
Sakataren kungiyar manoman ya yi kira ga gwamnati ta rika bayar da wannan rance tun kafin faduwar damina, domin manoma su rika cin gajiyar wannan shiri kamar yadda ya kamata.
Daga nan ya yi kira ga manoman shinkafa na ainihi a jihar Filato, su yi kokari su zo suyi rigista da wannan kungiya, don cin gajiyar wannan shiri.