MASU SUKAR SAYAWA BUHARI FOM BA MASU SON CI GABA BANE-GARKUWAN HAUSA FULANI
Isah Ahmed, Jos
WANI jigo a jam’iyyar APC reshen jihar Filato kuma Garkuwan al’ummar Hausa Fulani, na yankin Pengana da ke karamar hukumar Bassa a jihar ta Filato, Alhaji Ya’u Bala Jingir ya bayyana cewa duk masu sukar sayawa shugaban kasa, Muhammad Buhari fom na sake tsayawa takarar shugabancin kasar nan, ba masu son cigaban Nijeriya bane. Alhaji Ya’u Bala Jingir ya bayyana haka ne, a lokacin da yake zantawa da wakilinmu.
Ya ce maganar sayawa shugaba Buhari takardar fom ta sake tsayawa takarar shugaban kasa, ko shi kan sa ya yi al’kawarin bayar da kuxi naira miliyan 5 da dubu 500, don sayawa Buhari wannan fom, amma wata kungiya ta riga su wajen sayen wannan fom.
Alhaji Ya’u ya yi bayanin cewa babu shakka sun yi imanin cewa Buhari bashi da wadannan kudade naira miliyan 45, na sayen wannan fom. Kuma a tsari irin na Buhari ba zai dauki kudin gwamnati, ya sayawa kansa wannan fom ba. Domin shi adalin shugaba ne, mutumin kirki wanda yake kokarin ya hana cin hanci da rashawa a Nijeriya. kuma ya kawo cigaba da masu yawa, a shekaru uku da watanni da ya yi yana mulkin a Nijeriya.
Ya ce don haka ya ce shima zai bayar da naira miliyan 5 da dubu 500 wajen sayen wannan fom, kafin wannan qungiya ta saya masa. Ya ce amma tun da wannan qungiya sun riga sun sayawa Buhari fom, idan Allah ya kaimu anyi zabe yaci, zai shirya walima ya kira mutane.
‘’Wannan abu da wasu ‘yan Nijeriya suka yi, na sayawa Buhari fom ya nuna cewa ‘yan Nijeriya sun yarda cewa Buhari mai adalci ne, domin gashi a lokacin da yake can China, ga wasu sun saya masa takardar fom na sake tsayawa takara. Don haka duk masu suka kan sayawa Buhari fom, ba masu son cigaba Nijeriya bane. Kuma masu sukar Buhari basu da wani dalili na sukarsa, domin shi ba azalumi bane, kuma ba barawo bane’’.