Ziyarar Theresa May Ba Ya Yana Nufin Tsayar Da Buhari Bane – Hukumar Birtania

0
508

Daga Usman Nasidi

BABBAN hukumar kasar Birtaniya a Najeriya tace ziyarar da Theresa May, Fiaye Ministar Birtaniya ta kawo kwanan nan, ba yana nufin tsayar da Shugaban kasa Muhammadu Buhari kowani dan takara bane.

Laura Beaufils, mataimakiyar kwamishinan Birtaniya a Najeriya, ta bayyana hakan a jawabin da tayi a wani taron tattauanwa da hukumar ta shiryawa yan jarida a Lagas a ranar Juma’a.

Ta kuma bayyana jajircewar gwamanatin Birtaniya wajen kashe Euro miliyan 47.4 a shirin zurfafa damokradiyya a Najeriya

Da take Magana a kan rawar ganin da Birtaniya ke takawa wajen zurfafa damokradiyyar Najeriya, Beaufils ta bayyana cewa gwamnatin Birtaniya bata da kudirin sanya hannu a sakamakon zaben 2019, ta kara da cewa babu wani dan takara da tafi so.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here