Yan Shi\’a Sun Yi Zanga-Zanga A Kaduna Duk Da Haramcin Da Gwamnati Sanya Kan Haka

0
576

 

Daga Usman Nasidi

Kungiyar Musulman Shi’a a ranar Talata, 18 ga watan Satumba sun yi zanga-zanga kan cigaba da tsare shugaban su, Ibrahim El-zakzaky.

Mambobin kungiyar sun cigaba da zanga-zangarsu a Kaduna duk da haramcin da gwamnati ta sanya kan ayyukansu da sauran zanga-zanda a jihar.

Masu zanga-zangan sun fara zanga-zanga da misalin karfe 1:15 na rana sannan sunyi tattaki daga hanyar Poly zuwa Kasuwan Bacci dauke da kwalayen sanarwa, inda suke wakar “gwamnati ta saki Zakzaky” da ‘Allahu Akbar”.

Sai dai an lura da abu biyu, masu zanga-zangar basu yi amfani da bakaken kayan da aka sansu da shi ba sannan babu mata da yara a cikinsu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here