Daga Zubairu Abdullahi Sada
DAN takarar kujerar shugabancin Najeriya a jam\’iyyar PDP, Rt.Hon Aminu Waziri Tambuwal ya fadi cewa, muddin al\’ummar Najeriya suka ba shi goyo baya suka dora shi bisa kujerar shugabancin Najeriya, to, zai fuskanci matsalolin da suka shafi tsaro don samar da tabbataccen zaman lafiya musamman a yankunan arewa maso gabas da jihohi irin su Zamfara da Kaduna da ma fadin kasar nan baki daya.
Aminu Waziri ya ce, haka nana zai fuskanci kalubalen da ke addabar bangaren ilmi da na noma da kiwo da kiwon lafiyar dan Adam shi kansa, domin samar da lafiyayyun al\’umma da za su yi noman kuma \’ya\’yansu su sami ingantaccen ilmi a wajen malaman da suke da isasshen kwanciyar hankali babu zullumi a zukatansu.
Dan takarar ya ce, shi ba ya fito wannan takarar ba ne don kashin kansa, a\’a kira ne ya yi masa yawa wanda wajibinsa ya amsa kiraye-kirayen masoyansa, sannan sam ba shi da wata damuwa idan bai samu ya tsallake zaben share fage a jam\’iyyarsa ta PDP ba, zai goya wa duk wanda ya yi nasara baya don ganin an kai ga wannan kujera ta daya a fadin kasar nan.