An \’Ki Sayar Wa\’ Mata \’Yan Takara Fom A Zamfara?

    0
    643

     

    Rabo Haladu Daga  Kaduna

    WASU mata a jihar Zamfara sun koka kan kin sayar masu da fom din takara da jami\’iyyar APC ta yi a jihar.

    Daya daga cikin matan, Shafa\’atu Labbo mai neman tsayawa takarar majalisar jiha a mazabar Kaura ta Arewa, ta shaidawa manema labarai cewa ita da wasu mata biyu a jihar- Amina Iliyasu wacce ta nemi tsayawa takara a majalisar dokoki a mazabar Mafara/Anka da kuma Asabe Bala Kanoma wacce ta nemi tsayawa takara a majalisar jihar a mazabar Maru sun nemi tsayawa takarar ne karkashin jam\’iyyar APC.

    Ta ce a lokacin da a ka fara sayar da fom, jami\’yyar ta bayyana musu cewa ba ta shirya sayar da fom din \’yan majalisun dokoki da na jiha ba.

    \”Mun tanadi kudinmu mun yi ta zuwa sakatariyar APC amma sai aka yi ta yi mana yawo da hankali har zuwa lokacin da aka rufe sayar da fom din,\” in ji Shafa\’atu.

    Shafa\’atu Labbo ta ce jam\’iyyar ce ta bayyana musu cewa ba za a siyar da fom din masu son tsayawa takara a majalisa a Abuja ba, sai dai a jiha kuma za ta sanar da su idan lokaci ya yi.

    Ta ce ta yi kokarin yin magana da shugaban Jam\’iyyar APC na jihar Lawalli M. Liman don ta kai kukanta gareshi amma hakan bai yiwu ba,

    don kuwa bai amsa kiran da ta yi masa a waya ba sannan ta tura masa sako bai amsa ba Sai daga baya ne su ka ji rade-radin cewa ba za a sayar musu da fom din ba da gayya.

    Sai dai Shafa\’atu ta ce a yanzu jam\’iyyar ta fitar da jerin sunayen masu tsayawa takara kuma gaba dayansu maza ne.

    Ta ce akwai yiwuwar cewa gwamnan jihar Zamfara AbdulAzeez Yari na da wadanda ya ke so ya dora su tsaya takara a kujerun da su matan ke nema, shi ya sa a ka hana ita da sauran matan siyan fom din.

    Ta bayyana cewa abun da ya fi ba ta mamaki shi ne shugaban jam\’iyya na jihar Lawalli M Liman ne a ka tsayar a matsayin dan takara a kujerar da ta nema, wato dan majalisar jiha a mazabar Kaura ta Arewa.

    A cewar Shafa\’atu dai, wannan tsarin na gwamnan jihar ne, AbdulAzeez Yari.

    A kan haka, manema labarai  ta nemi jin ta bakin gwamnan kan wannan zargi, ta hanyar mai magana da yawunsa Ibrahim Dosara amma duk kokarin da muka yi don samunsa a waya ya citura.

    Sai dai sakataren jam\’iyyar APC na jihar ta Zamfara, Sani Mono ya musanta wannan zargi.

    Ya bayyana wa manema labarai cewa jam\’iyyar APC a Zamfara ba ta san da wannan zargi da Shafa\’atu Labbo ta ke yi mata ba.

     

    Ya ce \”Ai a Abuja a ka sayar da fom, me ya hana su je can su siya. Kuma abu ne da a ka siyar a bayyane ba a boye ba, don akwai tsarin da jam\’iyya ta fitar inda mai son tsayawa takara zai je banki ya biya kudi, sai ya kai takardar shaidar biyan kudin ga jami\’iyya a ba shi fom dinsa.\”

     

    Ya kuma ce an buga lambar asusun bankin a jaridu, don haka ba abu ne da a ka yi ba a boye ba.

    LEAVE A REPLY

    Please enter your comment!
    Please enter your name here