An Sace Ma\’aikatan Switzerland A Nigeria

0
684

 

Rabo Haladu Daga Kaduna

MASU fashi a tekun kasar Najeriya sun sace ma\’aikata 12 na wani jirgin ruwa mallakar kasar Switzerland.

A wata sanarwa da kamfanin dakon kaya na Massoel Shipping ya fitar, ya ce jirgin samfurin MV Glarus ya taso ne daga birnin Lagos , zuwa birnin Fatakwal na yankin Niger Delta mai arzikin mai.

Ma\’aikatan sun ce masu fashin sun shiga cikin jirgin ne kafin su sace mutanen, wanda ya ke dauke da Alkama sukai awon gaba da 12 daga cikin ma\’aikata 19.

Kamfanin ya ce ya na aiki tare da hukumomin Najeriya dan ganin sun kubutar da ma\’aikatan.

Haka kuma sojin ruwa da masu gadin teku ba su ce uffan kan sace m\’aikatan ba, amma tuni aka aike da kananan jiragen ruwa dan bin sahun \’yan fashin.

A dan tsakanin nan dai ana samun karuwar fashi a tekun Najeriya.

Haka a farkon watan Fabrairu masu fashin teku dauke da muggan makamai sun kai hare-hare biyu kan wasu jiragen ruwa mallakar kasashen waje.

Ko a watan Mayu da ya wuce an sace ma\’aikata 11 a Fatakwal kuma sai bayan makwanni biyu aka sako su.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here