Ba Zamu Amince Da Dauki Dora Ba – Biro Ka kiya

  0
  904

  Mustapha Imrana Abdullahi

  SAKAMAKON irin rikicin da jam\’iyyar PDP ke fama da shi a Jihar katsina ya haifar da tayar da hakarkarin wuya abin da yasa wadansu yayan jam\’iyyar bayyanawa duniya cewa ba za su amince da dauki dorar da ake kokarin yi masu ba.
  Wani jigo a PDP reshen Jihar Katsina Bashir Biro Kankiya ne ya bayyana hakan inda ya ce ba za su amince a yi masu dauki Dora Ba ta hanyar yi masu karfa karfar Nada masu wani Dan takara ba.
  Biro Kankiya ya ci gaba da cewa su abin da suka Sani shi ne ayi zaben deliget kawai ba wadansu mutane Tamanin su shiga daki su tsayar masu da wani Dan takara ba.
  \”Ko irin yadda aka yi mana lokacin da aka tsayar da Na shuni za a sake yi mana, Wanda dalilin hakan ya haifar wa PDP da ke da Gwamnati a lokacin matsalar kifewar Gwamnati a katsina\”.
  Ya kara da cewa za a ci gaba da tsayawa cak in har aka ce dauki Dora ko cushen wani Dan takara za a yi a PDP reshen katsina.
  \”Ta yaya muna cikin PDP tsawon lokaci sai a dauko masu wani haka kawai da ya shigo PDP daga Abuja ba a karbe shi a mazabarsa ba ace shi ne Dan takarar mu na Gwamnan Katsina? Ni PDP nake yi kuma Ina Goyon bayan Alhaji Ahmad Aminu Yar\’Aduwa da ke Neman kujerar Gwamnan Jihar katsina, don haka idan ba shi bane ni Bana yi Sam\”.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here