Mustapha Imrana Abdullahi Daga Kaduna
GABANIN zaben fitar da Yan takara a Jam\’iyyar APC da za a gudanar a ranar asabar, wadansu gungun Yan takarar da suke tunanin ba za a yi masu adalci ba a tsarin zaben deliget sun fito fili inda suke Kiran a canza batun deliget da yin zaben Kai tsaye na Kato bayan kato.
Wadannan Yan takara dai sun yi kira ga shugabannin APC na kasa da su shiga maganar domin a samu aiwatar da zaben Kato bayan Kato, Hajiya bayan Hajiya ko Malam bayan Malam tsarin da suka bayyana da cewa zai tabbatar da Dimokuradiyya.
Yan takarar da suka yi wannan Kiran lokacin da suna ganawa da manema labarai a Kaduna sun ce idan ba a dawo daga rakiyar yin wannan zabe na deliget ba za su yi kira ga uwar jam\’iyyar ta kasa da ta yi watsi da sakamakon zaben domin suma ba za su amince da shi ba.
Kamar yadda suka bayyana cewa zaben deliget ba zai samar da sahihan ingantattun Yan takarar da za su karbu wurin jama\’a masu zabe ba, don haka suke kara ankarar da uwar jam\’iyyar da sauran yayan ta su Sani cewa duk Wanda aka zaba ta hanyar zaben deliget hakika zai fadi a zaben gama Gari a Jihar kaduna.
Da yake jawabi a madadin sauran Yan takara a lokacin taron manema labaran da aka gudanar a cibiyar manema labarai ta kaduna, Hassan Danjuma Haruna da ake wa lakabi da \”sai Sandi\” Wanda yake takarar kujerar Dan Majalisar wakilai ta tarayya domin ya Wakilci mazabar Kaduna ta Arewa ya bayyana zaben deliget a matsayin Damfara da zamba cikin aminci don haka ya ki amincewa da yin wannan zabe na deliget kuma ya yi kiran a rushe shugabannin jam\’iyyar na Jiha.
\”Amma abin mamaki a lokacin taron masu ruwa da tsakin da aka gudanar a Abuja an kasa Jin ta bakin kowa sai daga bangaren Gwamnati kawai Wanda mataimakin Gwamnan Kaduna ya yi magana a madadin su.Kuma an yi ta yayatawa cewa an rigaya an amince a wurin taron cewa za a gudanar da zaben deliget Wanda ba haka abin yake ba.
\”Mataimakin Gwamna wannan magana ba haka take ba don haka da sake Babu inda aka amince da wannan mataki ko matsayar da kake cewa an amince da ita.Don haka babban abin da za a yi shi ne tattaunawa kawai a lalubo mafita kuma itace zaben Kai tsaye da jama\’a masu Karin Jam\’iyya za su aiwatar.
\”Zamu ci gaba da zama cikin jam\’iyyar kasancewar mun amince da tsari da kuma tanaje tanajen ta\”, don haka zamu ci gaba da zama a cikinta ba canji.