Rabo Haladu Daga. Kaduna
KWAMITIN gudanarwa na kasa na jam\’iyyar APC ya amince da tsarin zaben fitar da gwani na \’yan takarar gwamna da za a yi ranar Asabar, 29 ga watan Satumba a jihohin 36.
Tsarin dai ya kasu kashi biyu ne, na zabe kai tsaye, wanda ake kira kato bayan kato da kuma wanda ba na kai tsaye ba wato wanda wakilai ne wadanda ake kira deleget (delegates) za su yi.
Sai dai kuma a wata sanarwa da jam\’iyyar ta fitar mai dauke da sa hannun mukaddashin sakatarenta na watsa labarai, Mista Yekini Nabena, ta ce kwamitin na kasa ya haramta wa \’yan kwamitin gudanarwa na jihar Adamawa yin zaben dantakarar gwamnan jihar walau a matsayin wakilai (deleget) ko kuma masu sanya ido a zaben.
An yi musu wannan haramcin ne saboda kamar yadda kwamitin na kasa ya ce sun karkata ga bangaren wani daga cikin masu neman takarar.
Ga jerin yadda kowa ce jiha ta zabi tsarin da za ta bi wajen fitar da \’yan takarar wanda kuma kwamitin tarayyar ya amince: Zaben kai tsaye
1- ABIA
2- AKWA IBOM
3- ANAMBRA
4- BAUCHI
5- BAYELSA
6- CROSSRIVER
7- EDO
8- EKITI
9- IMO
10- KANO
11- LAGOS
12- NIGER
13- OGUN
14- ONDO
15- OSUN
16- TARABA
17- ZAMFARA
Zaben Deleget
1- ADAMAWA
2- BENUE
3- BORNO
4- DELTA
5- EBONYI
6- ENUGU
7- GOMBE
8- JIGAWA
9- KADUNA
10- KASTINA
11- KEBBI
12- KOGI
13- KWARA
14- NASARAWA
15- OYO
16- PLATEAU
17- RIVERS
18- SOKOTO
19- YOBE